'Zan Kashe Waya Ta': Gwamna ga Masu Neman Kawo Yaransu a ba Su Kwamishinoni
- Gwamna Umo Eno na Jihar Akwa Ibom ya karyata jerin sunayen kwamishinoni da aka wallafa, ya ce jerin ba gaskiya ba ne
- Gwamna Eno ya bayyana cewa mako mai zuwa zai gabatar da jerin sunayen gaskiya ga Majalisar Dokokin Jihar Akwa Ibom don tantancewa
- Gwamnan ya gargadi masu neman shiga majalisar zartarwa da kada su nemi matsayi ta hannun wasu mutane don ba su dama, ya ce hakan ba zai yi tasiri ba
- Wannan na zuwa ne bayan an sanar da cewa gwamnan ya sallami dukan mambobin Majalisar zartarwa a makon da ya gabata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Uyo, Akwa Ibom - Gwamna Umo Eno na Jihar Akwa Ibom ya bayyana jerin sunayen sabbin kwamishinoni da aka fitar a kafafen sadarwa a matsayin karya wanda ba shi da tushe.
Gwamnan ya fayyace hakan ne bayan yada wasu sunaye da bai san da su ba cewa su ne sababbin kwamishinoninsa inda ya gargadi masu ruwa da tsaki.
Gwamna ya fadi ranar fitar da kwamishinoni
A yayin da ya ke jawabi a liyafar bankwana ga tsofaffin mambobin majalisar zartarwa inda ya ce sun gama aikinsu, cewar rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Eno ya kara da cewa mako mai zuwa zai gabatar da jerin sunayen gaskiya ga Majalisar Dokokin Jihar don tantancewa da tabbatar da sababbin kwamishinoni.
Gwamnan ya nuna takaicinsa game da masu neman matsayi ke amfani da hanyoyin neman goyon bayan mutane masu tasiri, ya ce hakan ya ruguza musu dama.
Gwamna Eno ya gargadi masu ruwa da tsaki
A taron bankwana na karshe, tsofaffin mambobin majalisar zartarwar sun yanke shawara tare da amincewa kan korar dukan kwamishinoni, The Sun ta ruwaito.
Gwamnan ya yi gargadin cewa kada wani ya nemi ya tuntube shi domin neman matsayi, zai samu lambarsa a kashe har zuwa lokacin sanarwa ta gaba.
Ya bayyana cewa zai yi amfani da cancanta da amana wajen zabar sababbin mambobin majalisar zartarwa, wadanda za su kasance masu biyayya ga gwamna kadai.
Gwamna ya godewa tsofaffin kwamishinoni a jiharsa
Gwamnan ya bayyana cewa ayyukan raya jihar za su fara a watan Maris din 2025 kuma sababbin kwamishinoni za su fuskanci aiki mai matukar muhimmanci.
Ya jinjina wa tsofaffin mambobin majalisar zartarwa bisa gudunmawar da suka bayar wajen cikar manufofi da nasarorin gwamnatinsa.
Gwamna Eno ya tabbatar da cewa tsofaffin mambobin majalisar zartarwa ba su rasa komai ba, ya ce za a sake amfani da su a wasu matakai masu muhimmanci nan gaba.
Akwa Ibom: Gwamna ya rusa majalisar zartarwa
A baya, kun ji cewa Gwamnan Akwa Ibom, Fasto Umo Eno ya rusa majalisar zartarwa ta jihar a wani mataki na kawo gyara da sababbin dabaru a gwamnatinsa.
Umo Eno ya ce kwamishinonin sun yi bakin ƙoƙarinsu kuma babu wani daga cikinsu da ya aikata laifin da ya cancanci a kore shi.
An ruwaito cewa galibin kwamishinonin sun shafe shekaru 10 zuwa sama a ofis tun daga gwamnatin tsohon gwamna, Udom Emmanuel.
Asali: Legit.ng