Abin na Gida ne: Kanin Tsohon Gwamna Ya Shirya Neman Kujerar Yayansa da Ya Bari

Abin na Gida ne: Kanin Tsohon Gwamna Ya Shirya Neman Kujerar Yayansa da Ya Bari

  • Wani jigo a jam’iyyar PDP, Emmanuel Fayose, ya bayyana niyyarsa ta tsayawa takarar gwamna a Ekiti domin farfado da jihar da kawar da mulkin APC
  • Dan siyasar wanda ya kasance kanin tsohon gwamna, Ayodele Fayose ya nuna damuwa kan yadda jihar ta tsinci kanta a ciki bayan halin da APC ta jefa ta
  • Fayose ya ce manufarsa ita ce kifar da gwamnatin Oyebanji da gudanar da mulki mai hada kan kowa don inganta cigaban jihar Ekiti
  • Duk da batutuwan da suka shafi ganawar dan uwansa da Bola Tinubu, Fayose ya ce tsayuwarsa takara ba za ta shafi goyon bayan yan Ekiti ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Ado-Ekiti, Ekiti -Wani jigo a jam’iyyar PDP, Emmanuel Fayose, ya bayyana cewa zai shiga takarar gwamna a jihar Ekiti domin kawo sauyi da ci gaba.

Kara karanta wannan

'Ko a jikinmu': Gwamnan APC kan hadakar jam'iyyun adawa, ya fadi dabarbarun da za su yi

Fayose, kanin tsohon gwamnan jihar Ayodele Fayose, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai ranar Juma'a 10 ga watan Janairun 2025.

Kanin Fayose ya fara neman takarar gwamna a Ekiti
Kanin tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose ya shirya neman kujerar Gwamna. Hoto: Emmanuel Fayose.
Asali: Facebook

Kanin tsohon gwamna ya fara neman kujerar

A cewarsa, manufarsa ita ce farfado da jihar Ekiti da mayar da ita kan tafarkin ci gaba da inganta rayuwar al’umma, cewar jaridar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Na shiga takara ne don kifar da gwamnatin Oyebanji, sannan zan yi mulki mai hada kan kowa idan na samu nasara.”

- Emmanuel Fayose

Dan siyasar ya bayyana cewa haduwarsa da shugaban kasa Bola Tinubu ba za ta shafi kudurinsa na tsayawa takara ba.

Duk da cewa tsohon gwamna Ayodele Fayose ya ce zai goyi bayan gwamna mai ci, Emmanuel Fayose ya ce ba za a raunana shi ba.

Emmanuel ya fadi shirinsa kan jihar Ekiti

“Haduwar ‘dan uwana da Tinubu ba ta da wata alaka da kudurina domin muna da manufofi daban-daban kuma ba zan ja da baya ba.”

Kara karanta wannan

Menene gaskiyar labarin DSS sun kama Peter Obi? tsohon gwamnan ya fede gaskiya

“Zan ci gaba da neman sauyi ga jihar mu, kuma ina kira ga dukkan magoya bayana da su zama masu juriya."

- Cewar dan siyasar

Emmanuel Fayose ya shawarci mabiyansa a Ekiti

Fayose ya yi kira ga magoya bayansa da su ci gaba da kasancewa masu jajircewa domin PDP ta karbe mulki daga hannun APC mai ci a zaben 2026.

Ya kara da cewa jam’iyyar PDP za ta dawo da martabar jihar tare da inganta rayuwar al’ummar Ekiti nan gaba bayan shafe shekaru suna shan wahala a hannun APC.

Kanin Fayose ya fasa kwai kan alakarsu

A wani labarin, kun ji cewa kanin tsohon gwamnan Ekiti, Isaac Fayose ya sake kunto wata ta'asa inda ya ce yayansa Ayodele Fayose bai taba ba shi kwangila ba.

Isaac ya musanta zargin da ake yaɗawa cewa ya yi kudi ne lokacin da Ayodele Fayose ke mukin jihar Ekiti inda ya ce arzikinsa bai da alaƙa da dan uwansa.

Daga bisani, Isaac ya ware N50m a matsayin tukuici ga duk wanda ya nuna kwangilar da ya samu a gwamnatin Fayose musamman a lokacin da yake mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.