APC Ta Kamo Mai Nauyi, Kwamishinan Abba Ya Yi Sallama da NNPP da Kwankwasiyya
- Abbas Sani Abbas ya rabu da jam’iyyar NNPP da ta taimaka masa har ya zama kwashina a jihar Kano
- A lokacin da ya je gidan Sanata Barau Jibrin, ‘dan siyasar ya sauya sheka zuwa APC mai mulkin Najeriya
- Jibrin ya tabbatar da cewa tsohon kwamishinan ya hakura da dawainiya da jar hula da tafiyar Kwankwasiyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kano - Zaman Abbas Sani Abbas a jam’iyyar NNPP mai alamar kayan marmari ya zo karshe bayan ya rasa mukaminsa a jihar Kano.
An tabbatar da Hon. Abbas Sani Abbas ya koma gidan siyasar Barau Jibrin da jam’iyyar APC a ranar Juma’a, 10 ga watan Junairu 2024.
Barau ya karbi tsohon kwamishinan Abba
A shafin Facebook, mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Barau Jibrin ya shaida cewa ya karbi Honarabul Abbas Sani Abbas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abbas Abbas ya na cikin kwamishinoni biyar da Abba Kabir Yusuf ya sallama da ya yi garambawul a majalisar zartarwa kwanan nan.
Abbas ya rike kwamishinan cigaba da raya karkaka a gwamnatin Abba Kabir Yusuf a Kano.
Barau Jibrin ya shaida cewa sun yi maraba da ‘dan siyasar cikin APC mai mulkin kasa.
"Na yi maraba da Abbas Sani Abbas cikin babbar jam’iyyarmu ta APC a dan lokuta kadan da suka wuce.
"Ya kasance kwamishinan cigaba da raya karkara a jihar Kano har zuwa watan da ya gabata.
"Yayin da ziyarci gidana a Kano, a yau ya sanar da cewa ya fice daga jam’iyyar NNPP, ya shigo APC."
- Barau Jibrin
Dan Sarki sun karbi Abbas a jam'iyyar APC
Jawabin gwamnan ya bayyana cewa Abdullahi Abbas (Ɗan Sarki, Jikan Sarki), ya na cikin wadanda suka karbe shi a APC.
Abdullahi Abbas ya shafe shekara da shekaru yana jagorantar jam’iyyar APC a jihar Kano.
Daily Nigerian ta rahoto labarin inda aka ji mataimakin shugaban majalisar dattawan ya na alkawarin aiki tare da Hon. Abbas.
Barau Jibrin ya bayyana tsohon kwamishinan da rikakken ‘dan siyasa da yake da jama’a kuma da alama zai yi amfani a 2027.
Jibrin ya yi masa alkawarin cewa za su yi aiki tare wajen cigaban Kanawa da Najeriya.
A jawabin da ya fitar, Sanata Jibrin wanda ake ganin zai nemi takarar gwamnan Kano a 2027 ya ce za su cigaba da tafiya tare da kowa.
Tun ba yau ba dai Sanatan na Kano ta Arewa yake yi wa NNPP dauki daya-daya a jihar Kano, abin da ya jawo surutu sosai a yankin.
Hadimin Abba ya tabo Aminu Ado Bayero
A safiyar Asabar aka rahoto cewa wani mai ba gwamnan jihar Kano shawara ya hango karshen rigimar sarautar da ake ta faman yi.
Alhaji Hassan Sani Tukur bai ganin Aminu Ado Bayero zai kawo karshen sarautar Muhammadu Sanusi II, sai da ya ji kunya kawai.
Hadimin gwamna Abba Gida Gida ya ce za a bar Sarki Aminu Ado yana cizon yatsa idan an gama shari’ar da za ta iya kai wa kotun koli.
Asali: Legit.ng