"Zan Tona Asirinsu," Tsohon Sakataren Gwamnatin Abba Gida Gida Ya Dauki Zafi

"Zan Tona Asirinsu," Tsohon Sakataren Gwamnatin Abba Gida Gida Ya Dauki Zafi

  • Tsohon SSG, Dr. Abdullahi Baffa Bichi, ya yi barazanar bayyana bayanai masu zafi kan Gwamna Abba Yusuf da jagoran Kwankwasiyya
  • Dr Bichi ya zargi Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da Abba Gida Gida da cin amanarsa, inda ya ce zai bayyana gaskiya a kan jagororin biyu
  • Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya ce yana yana da takardu, bidiyo, da sautin murya da za su nunawa jama'a su waye Kwankwaso da Abba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Tsohon sakataren gwamnatin Kano, Dr. Abdullahi Baffa Bichi, ya yi barazanar tona asirin wasu da ake zargin gwamna Abba Kabir Yusuf, da Rabi’u Musa Kwankwaso ne.

Dr. Bichi ya bayyana cewa zai aiwatar da wannan manufa ta sa "a lokacin da ya dace," jim bayan an sallame shi daga mukaminsa bisa dalilan rashin lafiya.

Kara karanta wannan

Ya na ji ya na gani: Dalilai 5 da za su iya hana gwamnan APGA samun tazarce a 2025

AB Baffa
Baffa Bichi ya fusata bayan raba shi da mukamin sakataren gwamnatin Kano Hoto: AB Baffa/Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa Dr. Bichi ya bayyana matsayinsa ne yayin wani taro da magoya bayansa ranar Alhamis, bayan dawowarsa daga Saudiyya,.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan ne karon farko da ya yi magana tun bayan sallamarsa daga ofis tare da wasu kwamishinoni biyar a watan Disamba 2024, inda gwamnati ta bayyana cewa zai ba shi damar neman lafiya.

"Sun ci amanata," Abdullahi Baffa Bichi

A bidiyon da Na'allazi Bichi ya wallafa a shafin Facebook, Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya bayyana wasu 'yan siyasa a matsayin shugabanni masu yaudara da rashin amana.

“Na yi farin ciki cewa na kammala wa’adina cikin salama. Kamar yadda kuka sani, ba wannan ne lokacin da ya dace da yin magana ba, amma a lokacin da ya dace za mu bayyana gaskiya don mutane su gane irin mutanen da suke.”
“Ba mutanen da za a yarda da su ba ne... suna da mugun hali na yaudara da cin amana. Ba su da wata kwarewa face yaudara da rashin gaskiya.”

Kara karanta wannan

Ganduje ya karbawa kakakin APC da za a 'kashe' fada, ya zafafa kalamai ga Obi

"Ina da hujjoji a kansu" Inji Dr. Bichi

Tsohon Sakataren Gwamnatin Kano ya sha alwashin bayyana wasu bayanai masu zafi game da abokan siyasar sa da ake tsammanin Sanata Kwankwaso da Abba Gida Gida ne.

Ya ce yana da takardu, bidiyo, da sautin murya da ke nuna wasu abubuwan da ke da nasaba shugabannin bayan dakatar da shi daga NNPP da kora daga gwamnatin Kano.

Dr. Bichi ya ci gaba da cewa:

“Mun rubuta komai, muna da dukkan hujjoji daga takardu zuwa sautin murya da bidiyo.”

Jam'iyyar NNPP ta dakatar da Baffa Bichi

A baya, mun ruwaito cewa tun kafin a sallame shi daga mukamin SSG, reshen jam’iyyar NNPP na jihar Kano ya dakatar da Dr. Bichi bisa zargin rashin biyayya ga jam’iyya da shugabancinta.

An kuma samu rashin jituwa tsakanin Dr. Bichi da jagoran Kwankwasiyya, Kwankwaso, bayan ya fara jagorantar wata kungiyar siyasa da aka sani da Abba Tsaya da Kafarka.

Kara karanta wannan

Faransa ta yi magana kan zargin hada kai da Najeriya ta yamutsa Nijar

Ana zargin Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya na daga cikin manyamanyan da suke jagorantar tafiyar, wadda ke neman Gwamna Abba Kabir Yusuf ya raba hanya da jagorarsa ta siyasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.