'Mun Gano Shi': Shugabannin PDP Sun Tabbatar Gwamna Zai Koma APC, Sun Jero Dalilai

'Mun Gano Shi': Shugabannin PDP Sun Tabbatar Gwamna Zai Koma APC, Sun Jero Dalilai

  • Wasu shugabannin PDP a jihar Delta sun yi magana kan jita-jitar cewa Gwamna Sheriff Oborevwori zai koma APC mai mulkin Najeriya
  • Shugabannin suka ce gwamna Oborevwori na shirin sauya sheƙa zuwa APC, duk da musantawa daga mukarrabansa suka yi ta yi a kwanakin nan
  • Wasu rahotanni sun nuna gwamna ya fara tattaunawa da shugabannin APC, har da wata tafiya mai rikitarwa zuwa ƙasar Ghana da Bola Tinubu
  • Kungiyar Concerned Leaders ta PDP ta ce wannan mataki na iya girgiza tsarin siyasar Delta, tana neman gwamna ya bayyana gaskiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Asaba, Delta - Wasu shugabannin jam'iyyar PDP a jihar Delta sun magantu kan zargin shirin Gwamna Sheriff Oborevwori na komawa APC mai mulkin Najeriya.

Shugabannin suka ce ana zargin gwamnan yana shirin sauya sheƙa daga PDP zuwa APC, duk da musantawa daga wasu mukarrabansa suka yi da cewa labarin karya ne.

Kara karanta wannan

Ya na ji ya na gani: Dalilai 5 da za su iya hana gwamnan APGA samun tazarce a 2025

An gano shirin gwamnan PDP da ke niyyar komawa APC
Wasu shugabannin PDP sun tabbatar da cewa gwamna zai koma APC. Hoto: Sheriff Oborevwori.
Asali: Twitter

Wasu shugabannin PDP sun zargi Gwamna Oborevwori

Kungiyar Concerned Leaders of PDP a Delta ta ce gwamna Sheriff yana shirin barin PDP saboda wasu shirye-shirye da yake yi, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da Theophilus Ekiyo da Ochuko Oghenekome da kuma Ezekiel Chukwudi suka sanya wa hannu.

"Gwamnan yana shirin barin jam’iyyarsa ta PDP domin shiga sabuwar jam’iyya, kuma ya fara tattaunawa da shugabannin APC."

- Cewar sanarwar

Ana zargin Gwamna ya gana da Tinubu

Kungiyar ta ce wannan lamari zai iya kawo sauyi a siyasar Delta, musamman idan aka tabbatar da jita-jitar sauya sheƙar wanda alamu duk sun nuna hakan.

Duk da musantawa daga mai magana da yawun gwamna, Festus Ahon, da shugaban PDP na jihar, Solomon Arenyeka, alamu suna nuna akwai kamshin gaskiya.

An tabbatar gwamna ya gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a tafiyarsu zuwa Ghana wanda ya ƙara jawo tambayoyi kan dalilin ziyarar.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban AMAC ya sauya sheƙa zuwa APC, ya shiga takarar gwamna

Kungiya ta kalubalanci Gwamna kan shirin komawa APC

Kungiyar ta tambayi dalilin halartar gwamna wajen taron ƙasashen waje idan ba don shirya barin jam'iyyar PDP ba ne.

Har ila yau, ƙungiyar ta bayyana hakan a matsayin cin amanar jam'iyyar da ta ɗora gwamna kan mulki duba da wahalar da ƴaƴanta suka sha tun kafin zuwansa.

Kungiyar ta yi kira ga 'yan PDP su kasance masu sa ido tare da neman gwamna ya yi wa al'umma bayani game da matakinsa na siyasa.

Ana zargin wasu gwamnoni za su koma APC

Kun ji cewa rahotanni sun nuna cewa ana zargin wasu daga cikin gwamnonin PDP na shirin barin jam’iyyar domin komawa APC mai mulki saboda rikice-rikice da suka addabe ta.

Wasu majiyoyi suka ce ana zargin cewa akwai wasu gwamnonin PDP da suka fara ziyartar shugaba Bola Tinubu a Lagos domin tattaunawa kan siyasa da wasu lamura.

Wasu kungiyoyi a jihar Delta da ke Kudancin Najeriya sun bukaci Gwamna Sheriff Oborevwori ya fitar da sanarwa game da jita-jitar cewa yana shirin barin PDP zuwa APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.