Ya na Ji Ya na Gani: Dalilai 5 da Za Su Iya Hana Gwamnan APGA Samun Tazarce a 2025

Ya na Ji Ya na Gani: Dalilai 5 da Za Su Iya Hana Gwamnan APGA Samun Tazarce a 2025

  • Gangar siyasa ta fara kadawa yayin da wa’adin farko na Chukwuma Charles Soludo a matsayin gwamnan Anambra ya zo karshe
  • A 2025, al’ummar Anambra za su koma rumfunan zabe domin sake zaben Gwamna Soludo ko kuma su goyi bayan wani sabon shugaba
  • Kafin zaben na 2025, matsalolin siyasa sun fara bayyana, inda Legit Hausa ta zakulo dalilai biyar da ka iya hana Gwamna Soludo tazarce

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Anambra - Magoya bayan Charles Soludo, gwamnan Anambra sun sha cewa ba shi da abokin hamayya a zaben 2025, amma yanzu ana ganin komai na iya faruwa.

Tun daga rikicin harkokin addini da Gwamna Soludo ya jefa kansa, har zuwa ga barazanar jam'iyyun adawa, ana ganin zai sha bakar wahala a neman tazarcensa a 2025.

Rahoto ya yi bayanin irin kalubalen da gwamnan Anambra zai fuskanta a zaben 2025
Gwamna Charles Soludo na iya fuskantar matsala a zaben gwamnan jihar Anambra na 2025. Hoto: Charles Chukwuma Soludo
Asali: Facebook

A cikin wannan rahoto, Legit.ng Hausa ta hasko wasu dalilai biyar da za su iya zama sanadiyyar da Gwamna Soludo zai rasa tazarce a 2025.

Kara karanta wannan

'Ko a jikinmu': Gwamnan APC kan hadakar jam'iyyun adawa, ya fadi dabarbarun da za su yi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Siyasar addini

Tun a shekarar 1999 siyasar addini ta kasance mai tasiri a Anambra, inda majimi'u da kuma bangarorin addinin Kirista ke taka rawa wajen zaben wanda zai zama gwamna.

Idan ka cire Chinwoke Mbadinuju da aka zaba a 1999, kowane gwamnan Anambra yana kasancewa dan majami'ar Katolika ko kuma dan majami'ar Anglican.

Duk da cewa Gwamna Solodo dan darikar Katolika ne kuma mataimakinsa Onyekachi Ibezim dan Angilican ne, ana ganin za su fuskanci turjiyar addini a zaben 2025.

A farkon shekarar 2024, Gwamna Soludo ya samu sabani da limaman Cocin Katolika, inji rahoton This Day.

Gwamnan ya sake tsaurara dokar jana’iza da ta haramta gudanar da bukukuwan jana’iza a jihar Anambra wanda ya jawo sabanin tsakaninsa dacocin Katolika

Ana ganin mabiya darikar Katolika za su iya ba Sulodo matsala a zaben 2025 saboda ya taba zuriyar babban shugaba a majami'arsu.

2. Rikici kan zaben kananan hukumomi

Kara karanta wannan

Wani gwamnan PDP zai sauya sheka zuwa jam'iyyar APC? Gwamnati ta fito da bayani

‘Yan adawa sun soki zaben kananan hukumomin jihar Anambra da aka gudanar a 2024 yayin da jam'iyyar APGA ta lashe dukkanin kujerun ciyamomi 21, inji rahoton Punch.

Masu adawar sun ce Gwamna Soludo ya nuna rashin adalci ta hanyar murde zaben tare da tabbatar da cewa 'yan adawa ba su samu ko kujera daya ba.

Rikice-rikicen da suka biyo bayan wannan zaben har yanzu ba su lafa ba, kuma ana ganin za su iya yin tasiri kan gwamnan a wajen hana shi tazarce a 2025.

3. Zargin ƙoƙarin tadiyewa kananan hukumomi kafa

A watan Oktobar 2024, kusoshin jam’iyyar LP a majalisar tarayya suka zargi Gwamna Soludo da kokarin take hukuncin kotun koli kan ikon kananan hukumomi.

Duk da Gwamna Soludo ya nace cewa ba yana kokarin tauye ikon kananan hukumomi ba ne, hakan bai hana shi fuskantar caccaka daga 'yan adawar ba.

Kara karanta wannan

Gwamna ya canza sunan jami'a, ya raɗa mata 'Jami'ar Kashim Ibrahim'

A wani taron manema labarai Abuja, jagoran 'yan jam'iyyar LP a majalisar tarayyar, Sanata Tony Nwoye, ya zargi gwamnan da cin dunduniyar kananan hukumomi.

Sanata Nwoye ya nuna damuwa kan shirin gwamnan na kafa dokar haɗa asusun jiha da na kananan hukumomi duk da kotun koli ta hana hakan.

A cewarsa, wannan matakin yana nufin tadiyewa kananan hukumomi kafa kan ikon cin gashin kansu a bangaren kudi.

4. Raguwar karfin siyasar jam'iyyar APGA

Masana siyasa da dama sun yarda cewa karfin jam’iyyar APGA ya ragu a jihar Anambra, kuma ta rage karsashin da zai iya sa ta samu tazarce a 2025.

Tun bayan shekarar 2006 da APGA ta fara mulki a jihar Anambra, abubuwa da dama sun faru, kuma tushen da aka kafa jam’iyyar a kansa ya girgiza.

An ce hakan ya jawo an samu barazana da kuma haddasa rikice-rikice tsakanin masu ruwa da tsaki da dama a cikin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Dan Bilki Kwamanda: Abba ya hana ni zuwa aikin hajji duk da taimakon Kashim Shettima

5. Barazanar APC da jam'iyyar LP

Yayin da Gwamna Soludo ke fuskantar matsalolin cikin gida, a waje kuma salon siyasar da jam'iyyun adawa suka dauka ya kara ta'azzara al’amura gwamnan.

An ce sauya shekar Sanata Uche Ekwunife, babbar 'yar siyasa daga PDP zuwa APC, ya kara daukar hankali kan shirin APC na karbe mulki daga hannun Soludo.

Ko da yake, itama kanta APC ta na fama da rikice-rikicen cikin gida, amma an ce shigowar Ekwunife ya kara wa jam’iyyar kuzari.

Yayin da har yanzu ake yayin Peter Obi a Anambra, wasu suna ganin Valentine Ozigbo, wanda ya gwabza da Soludo a zaben da ya gabata, na iya sake samun takara.

Ana hasashen cewa wannan karon Valentine Ozigbo zai iya fitowa a jam’iyya LP bayan ficewarsa daga jam'iyyar PDP.

Charles Soludo ya soke zaben sabon sarki

Kara karanta wannan

'Zargin maita': Wasu fusatattun matasa sun bankawa mutumi wuta har lahira

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamna Charles Soludo na jihar Anambra ya sa baki a rikicin sarautar garin Oba, Idemili, wanda ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.

An ce Gwamna Soludo ya dakatar da zaɓen sabon sarki, haka nan ya kuma umarci jami'an tsaro da su kama duk wanda ya yi kunnen ƙashi da umarninsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.