"Mun Gamsu da Kai": Gwamna a Arewa Ya Samu Goyon Bayan Takara a Zaɓen 2027
- Gwamnan Taraba, Agbu Kefas ya fara samun goyon baya tun kafin ya ayyana takarar neman zango na biyu a zaɓen 2027
- Ƴan fansho na jihar Taraba sun bayyana gamsuwarsu da salon mulkin Kefas, sun ce ya cancanci ya samu wa'adi na biyu a zaɓe mai zuwa
- Shugaban ƙungiyar ƴan fansho watau NUP, Alhaji Mamudu Yoro ya ce gwamnan ya ɗaga ƙimar jihar Taraba a idon duniya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Taraba - Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba ya fara samun goyon baya daga al'umma game takarar neman tazarce da zai iya nema a zaɓen 2027.
Kungiyar ƴan fansho ta Najeriya (NUP) reshen Taraba, ta goyi bayan Gwamna Agbu Kefas ya nemi wa’adi na biyu a zaben gwamna mai zuwa a 2027.
Shugaban NUP na jihar, Alhaji Mamudu Famlak Yaro, ne ya bayyana hakan a wurin taron kaddamar da fara biyan haƙƙokin ƴan fasho a Jalingo, Tribune ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
2027: Gwamna Kefas ya samu goyon baya
Alhaji Mamudu ya bayyana cewa gwamnan ya nuna jajircewa wajen inganta rayuwar ma'aikatan da suka yi ritaya.
Ya ce wannan ne babban abin da ya sanya suka yanke shawarar mara masa baya tun yanzu domin ya yi shekara takwasa a kan mulki.
Shugaban ƴan fanshon ya ce jajircewar gwamna ta sa Taraba ta zo ta uku a jerin jihohin da suka fi kula da walwalar tsoffin ma’aikata a taron ƴan fansho na ƙasa da aka yi a Abuja.
Gwamnan Taraba ya damu da walwalar ƴan fansho
“Gwamna Agbu Kefas ya nuna ƙauna da damuwa ga walwalar ƴan fansho na ƙananan hukumomi da jiha.
"Saboda haka, muna da kwarin guiwar cewa idan ya samu damar wa’adi na biyu, zai ci gaba da inganta walwala da jin daɗin tsofaffin ma’aikata,” in ji Mamudu.
Mamudu Yaro ya kuma ƙara cewa gwamnan ya himmatu wajen kawo sauyi a bangarori da dama na gwamnati, wanda ya sa Taraba ta fara kere tsara a fagen ci gaba.
Ƴan fansho sun haɗa kansu a jihar Taraba
Har ila yau a wurin taron, Alhaji Mamudu nuna farin cikinsa da Kwamared Elnathan Bila Auta ya yi rijistar zama cikakken ɗan ƙungiyar ƴan fansho.
"Yanzu dai komai ya bayyana an share tantamar masu tunanin ƙungiyar NUP na da shugabanni biyu a Taraba.
"Elnathan Bila Auta wanda ke ikirarin shugabanci bai zama ɗan kungiya ba sai a yau."
Alhaji Mamudu ya kuma yaba da yadda gwamnatin Agbu Kefas ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na biyan tsoffin ma’aikata haƙƙoƙinsu da suka biyo bashi.
Wannan goyon baya ga ƴan fanshon Taraba ya nuna yadda Gwamna Kefas ke samun amincewa daga al’ummar jihar, musamman masu ritaya.
Gwamnan Taraba ya shirya gyara fannin ilimi
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Agbu Kefas ya jaddada aniyarsa na gyara fannin ilimi ta yadda ƴan Taraba za su samu damar iyin karatu cikin sauƙi
Agbu Kefas ya ce ilimi shi ne babban abin da gwamnatinsa ta sa gaba shiyasa ya maida karatun firamare da sakandire kyauta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng