'Ko a Jikinmu': Gwamnan APC kan Hadakar Jam'iyyun Adawa, Ya Fadi Dabarbarun da Za Su Yi

'Ko a Jikinmu': Gwamnan APC kan Hadakar Jam'iyyun Adawa, Ya Fadi Dabarbarun da Za Su Yi

  • Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce jam'iyyar APC ba ta da wani dalilin tsoro kan hadewar wasu jam'iyyun adawa da ake hasashe
  • Gwamna Sule ya bayyana cewa nasarar APC a matakin Tarayya da jihohi zai tabbatar da matsayinta na shugabanci a shekaru biyu masu zuwa
  • Gwamnan ya kara da cewa Bola Tinubu ya umarci gwamnoni su mayar da hankali kan bunkasa noma, fasahar sana’o’i, hakar ma’adanai da ci gaba a matakai daban-daban
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake cigaba da hasashen cewa jam'iyyun adawa suna ta shirye-shiryen hada kai domin tunkarar zaben 2027

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Lafia, Nasarawa - Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya yi magana kan hadakar jam'iyyun adawa kan zaben 2027.

Gwamna Sule ya bukaci jam'iyyar APC ta kwantar da hankalinta kan zancen hadewar wasu jam'iyyun adawa da ake hasashe.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fadi alakarsa da El-Rufai, ya magantu kan barinsa APC da hana shi Minista

Gwamnan APC ya magantu kan hadakar jam'iyyun adawa
Gwamna Abdullahi Sule ya ce ko kadan APC ba ta tsoron hadakar jam'iyyun adawa. Hoto: Atiku Abubakar, Peter Obi, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Gwamna ya fadi shirin APC a Najeriya

Gwamna Sule ya fadi haka ne yayin hira a gidan talabijin na Channels a daren jiya Laraba 8 ga watan Janairun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin hirar, Gwamna Sule ya bayyana cewa APC za ta yi abin a zo a gani a cikin shekaru biyu masu zuwa.

''Abin da za mu yi a cikin shekaru biyu masu zuwa zai tabbatar da matsayin jam'iyyar, kuma muna da yakinin nasara sosai."
''Idan muka yi hakan, ba zan ga wani dalilin da zai sa jam'iyyar APC ta ji tsoro kan wani hadewar jam'iyyun adawa ba."
'Cikin girmamawa, ba na jin tsoron komai, nasarar jam'iyya tana da nasaba da aiki ba kawai a Tarayya ba har ma a jihohi.''

- Abdullahi Sule

Umarnin Tinubu kan zaben 2027

Gwamna Sule ya ce zabe bai tsaya a matakin Tarayya kadai ba, ana gudanar da shi a jihohi, kananan hukumomi da sauran matakai daban-daban.

Kara karanta wannan

Abin da ya hana gwamnoni taimakon Malam El Rufai lokacin da aka naɗa shi minista

Ya ce Bola Tinubu ya umarci gwamnonin jihohi su tabbatar da cewa sun samar da ababan cigaba da tabbatar da nasarar APC.

"A wasu lokuta, mutane na mai da hankali kan manufofin Gwamnatin Tarayya, amma zabe na faruwa ne a matakin jiha da kasa baki daya."
"Shi ya sa shugaban kasa, a taronmu na ranar 1 ga Disamba, ya umarci gwamnoni su mayar da hankali kan cigaba a jihohinsu."

- Abdullahi Sule

Sule ya bayyana cewa shugaban kasa Tinubu ya jaddada muhimmancin noma, sana'o'in dogaro da kai, da inganta rayuwar mutane a jihohi.

Ya ce shugaban kasa yana mayar da alhakin cigaba ga jihohi, don haka shugabannin jihohi ne ke da nauyin ciyar da kasa gaba.

An fara shirin tumbuke Tinubu a 2027

Kun ji cewa jam’iyyun siyasa a a Najeriya na ci gaba da bayyana shirin fara zaben 2027 nan ba da dadewa ba, duk da sauran shekaru.

Kara karanta wannan

Wani gwamnan PDP zai sauya sheka zuwa jam'iyyar APC? Gwamnati ta fito da bayani

Jam’iyyun adawa a kasar na ci gaba da kokarin ganin sun hada kai domin tabbatar da an kwace mulki daga hannun shugaba Bola Tinubu.

Da yawa daga cikin jiga-jigan siyasar Najeriya na yiwa mulkin Bola Tinubu kallon akwai gyara a ciki, lamarin da ke daukar hankali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.