Gwamna Ya Fadi Alakarsa da El Rufai, Ya Magantu kan Barinsa APC da Hana Shi Minista
- Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya yi magana kan alakarsa da tsohon gwamna, Nasir El-Rufai da hana shi mukamin Minista
- Abdullahi Sule ya ce babu yadda za a shigo da matsalar nadin Nasir El-Rufai a matsayin Minista cikin ganawar gwamnonin APC
- Sule ya tabbatar da cewa Nasir El-Rufai bai fice daga jam’iyyar APC ba, duk da tsaikon nadin shi a watan Agustan 2023
- Hakan ya biyo bayan rawar da El-Rufai ya taka rawa wajen tabbatar da tikitin shugabancin APC ya koma Kudu a zaben 2023
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Lafia, Nasarawa - Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya magantu kan yanayin da ake ciki tsakaninsu da tsohon gwamna, Nasir El-Rufai.
Gwamnan ya ce yana da alaƙa mai kyau tsakaninsa da El-Rufai amma bai sake yin magana da shi ba tun bayan ya bar mulki.

Source: Facebook
Gudunmawar El-Rufai domin nasarar Tinubu a 2023
Gwamna Sule ya bayyana haka ne a daren jiya Laraba, 8 ga watan Janairun 2025 yayin hira da gidan talabijin na Channels.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
El-Rufai yana cikin jagororin Arewacin Najeriya da suka goyi bayan mika tikitin shugaban kasa na APC zuwa Kudu bayan kammala wa'adin Muhammadu Buhari.
Wannan matakin ya dace da tsarin karba-karba na mulki tsakanin yankunan Kudu da Arewa bayan wa’adin mulkin Buhari na shekaru takwas.
El-Rufai, wanda ya yi gwamna a jihar Kaduna daga 2015 zuwa 2023, ya nuna goyon baya ga tsohon gwamnan Lagos, Bola Tinubu, a matsayin dan takarar APC.
Gwamna Sule ya magantu kan hana El-Rufai Minista
Gwamna Sule ya ce ba za a iya shigar da gwamnonin APC cikin lamarin Nasir El-Rufai ba musamman kan hana shi mukamin Minista.
Gwamnan ya ce Nasir El-Rufai bai bar jam'iyyar APC ba, duk da cewa Majalisar Tarayya ta ki amincewa da nadinsa a watan Agustan 2023.
Gwamna ya kore maganar El-Rufai zai bar APC
“El-Rufai bai bar jam’iyyarmu ba, har yanzu yana cikin jam’iyyarmu, ya yi kusa a fara wannan magana."
“Tun da ya bar ofis, ban yi magana da El-Rufai ba, ban san inda yake ba, ko abin da yake yi ba.”
“Ban san komai game da motsinsa ba, amma na ga maganganu da barazanar mutane daban-daban, duk da haka lokaci bai yi ba.”
- Abdullahi Sule
El-Rufai ya gana da Al-Mustapha da jigon PDP
A baya, kun ji cewa ana ta hasashen hadakar jam'iyyun adawa a Najeriya musamman game da zaben 2027, manyan yan siyasa sun gana a birnin Tarayya Abuja.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi wata ganawa da Manjo Hamza Al-Mustapha da shugaban jam'iyyar SDP da jigon PDP, Otunba Segun Showunmi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa ganawar ba ta rasa nasaba da halin da kasa ke ciki da kuma shirye-shiryen jam'iyyun adawa kan zaben 2027 da Bola Tinubu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

