Abin da Ya Hana Gwamnoni Taimakon Malam El Rufai Lokacin da Aka Naɗa Shi Minista

Abin da Ya Hana Gwamnoni Taimakon Malam El Rufai Lokacin da Aka Naɗa Shi Minista

  • Gwamnonin APC ba za su iya taimakon tsohon gwamna Nasir El-Rufai ba a lokacin da Majalisa ta ki amincewa da naɗinsa a matsyain minista
  • Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ne ya bayyana hakan ranar Laraba, ya ce naɗin minista na hannun mai girma shugaban ƙasar Najeriya
  • Malam Nasiru El-Rufai na cikin manyan ƴan siyasa a Arewa da suka taimaki Bola Tinubu har ya zama shugaban ƙasa a lokacin da aka yi zaben 2023

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Nasarawa - Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce ƙungiyar gwamnonin APC ba ta da hurumin yin wani abu game da abin da ya faru da Malam Nasiru El-Rufai.

Gwamna Sule ya ce gwamnonin APC ba za su iya yin komai ba dangane da tangarɗar da aka samu lokacin naɗin tsohon gwamnan Kaduna, El-Rufa'i a matsayin minista.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fadi alakarsa da El-Rufai, ya magantu kan barinsa APC da hana shi Minista

Gwamna Abdullahi Sule.
Gwamna Sule ya ce gwamnonin APC ba za su iya komai ba a lokacin da aka ki amincewa da naɗin El-Rufai Hoto: Abdullahi A. Sule
Asali: Facebook

Abdullahi Sule ya bayyana haka ne a cikin shirin siyasa a yau na kafar talabijin ta Channels tv ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnonin APC sun faɗi dalilinsu kan El-Rufai

Ya kuma tabbatar da cewa har yanzu El-Rufai bai bar jam’iyyar APC ba duk da mataƙin Majalisa na kin amincewa da nadinsa a matsayin minista a watan Agusta 2023.

“El-Rufai bai bar jam’iyyarmu ba, har yanzu yana cikin APC. Dalilin naɗinsa da ƙin amincewar majalisa, ko kaɗan ba mu tattauna batun a kungiyar gwamnonin APC ko ƙungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) ba."
"Wannan ba abin da ya shafe mu ba ne, don haka ina ganin babu abin da za mu iya yi a kai," in ji Gwamna Sule.

Shugaban ƙasa ke da hurumin naɗa minista

Gwamnan ya ƙara da cewa shugaban ƙasa ke da ikon naɗa duk wanda ya ga dama kuma ya amince ya zama minista a gwamnatinsa.

Sannan a cewar Sule, Majalisar tarayya da wasu hukumomin tsaro su ke da alhakin tantancewa da tabbatar da naɗin minista.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya gargadi kwamishinoni, ya fadi abin da ba zai lamunta ba

Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai na daya daga cikin shahararrun ‘yan siyasa a Arewacin Najeriya.

Ya taka rawa wajen tabbatar da cewa tikitin takarar shugaɓan ƙasa na jam’iyyar APC a zaben 2023 ya koma yankin Kudu.

Wannan ya biyo bayan tsarin karba-karba tsakanin yankin Arewa da Kudu, wanda ake amfani da shi a siyasar Najeriya.

Tsohon gwamnan Kaduna ya taimaki Tinubu

A lokacin mulkin Muhammadu Buhari, El-Rufai ya yi kokari wajen tallafawa tsohon gwamnan Legas, Bola Ahmed Tinubu, wanda daga bisani ya zama dan takarar APC kuma ya lashe zaben 2023.

Tsohon gwamnan Kaduna, wanda ya yi mulki daga Mayu, 2015 zuwa Mayu, 2023, ya fito fili ya marawa Tinubu baya, duk da cewa akwai wasu manyan ‘yan takara daga Arewa.

Gwamna Sule ya tabbatar da cewa har yanzu Malam El-Rufai na nan a cikin jam'iyyar APC duk da matsalar da aka samu wajen naɗinsa a matsayin minista.

Kara karanta wannan

'Magana ta fara fitowa': Hamza Al Mustapha ya fadi dalilin ganawa da El Rufa'i

Gwamna Sule ya goyi bayan kudirin haraji

A wani labarin, an ji cewa Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana goyon bayansa ga kudurin sauya fasalin harajin shugaban ƙasa, Bola Tinubu.

Gwamna Sule, wanda a baya ya soki kudirin ya ce an masa ƙarin bayani kuma ya fahimci duk abin da ke cikin sabon tsarin harajin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262