Menene Gaskiyar Labarin DSS Sun Kama Peter Obi? Tsohon Gwamnan Ya Fede Gaskiya
- Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter Obi ya yi martani kan jita-jitar cewa hukumar DSS ta kama shi a birnin Abuja
- Obi ya karyata rahotannin da ke cewa an kama shi a Abuja, yana mai cewa labarin "karya ce tsagwaronta" kuma babu gaskiya a ciki
- Tsohon gwamnan Anambra ya bayyana cewa yana gidansa a Onitsha tare da yin kira ga ‘yan Najeriya su kauracewa yada jita-jita marasa tushe
- Peter Obi ya yi tir da irin yada bayanan karya a kansa, yana cewa hakan ba zai hana shi cigaba da neman ingantacciyar Najeriya ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi ya fayyace gaskiya kan rahotanni da ke yaɗawa cewa an kama shi a birnin Tarayya, Abuja.
Dan takarar shugaban kasa a LP ya musanta labarin cewa an kama shi inda ya ba yan Najeriya shawara kan haka.
Peter Obi ya musanta labarin cafke shi
Peter Obi ya fitar da wannan sanarwar ne ta shafinsa na X a yau Laraba 8 ga watan Janairun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A shafukan sada zumunta, musamman X, an ruwaito cewa DSS sun kama Obi a gidansa da ke Abuja inda suka kai shi wani wurin da ba a sani ba.
Obi ya musanta wannan rahoto kwata-kwata, yana mai cewa, 'wannan labari duk karya ne kuma babu gaskiya a cikinsa'.
Obi ya fadi inda yake a halin yanzu
Tsohon gwamnan ya kuma bayyana cewa yana gidansa a Onitsha da ke jihar Anambra, yana cigaba da rayuwarsa ba tare da wata matsala ba.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a 2023 ya yi Allah wadai da yada jita-jita marasa tushe da ke fitowa a kansa.
"Tun bara a watan Satumba lokacin da nake Rwanda, irin wannan karyar ta fito cewa DSS sun mamaye gidana, yanzu kuma haka ake fada."
"Manufar masu irin wannan jita-jita ba ta da kyau, amma ya kamata mu maida hankali kan matsalolin da Najeriya ke fama da su."
- Peter Obi
Peter Obi ya fadi fatansa kan Najeriya
Peter Obi ya bayyana cewa manufofin masu yada irin wadannan jita-jitar ba su da kyau, yana kira ga ‘yan Najeriya su yi watsi da su.
Obi ya gode wa jama’a bisa goyon bayan da suke nuna masa, yana mai cewa yana nan daram wajen neman ingantacciyar Najeriya ga kowa da kowa.
Atiku ya shiga fadan Peter Obi da Tinubu
Kun ji cewa dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar ya shiga rigima tsakanin gwamnatin Bola Tinubu da Peter Obi.
Atiku ya ce maganganun kakakin jam'iyyar APC mai mulki, Felix Morka a kan Peter Obi, sun nuna wata alama ta rashin yarda da 'yancin masu adawa.
Ya ce kalaman da suka nuna Obi ya "ketare iyaka" sun bayyana rashin girmamawa ga dimukradiyya da muhimmancin muhawara mai amfani.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng