Ganduje da APC Sun Yi Babban Kamu, Tsohon Shugaban PDP Ya Koma Jam'iyya

Ganduje da APC Sun Yi Babban Kamu, Tsohon Shugaban PDP Ya Koma Jam'iyya

  • Jam'iyyar APC mai adawa a jihar Abia ta samu ƙaruwa bayan wani babban jigo a siyasance ya sauya sheƙa zuwa cikinta
  • Tsohon shugaban PDP a jihar Abia, Sanata Emma Nwaka, ya rungumi tafiyar tsintsiya bayan ya koma jam'iyyar APC
  • Komawar Sanata Nwaka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya na zuwa ne watanni shida bayan ya yi murabus daga PDP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Abia - Tsohon shugaban jam'iyyar PDP a jihar Abia, Sanata Emma Nwaka, ya koma jam'iyyar APC.

Sanata Emma Nwaka ya koma jam'iyyar APC ne watanni shida bayan ya yi murabus daga PDP.

Tsohon shugaban PDP ya koma APC a Abia
Sanata Emma Nwaka ya koma APC a Abia Hoto: @OfficialAPCNg (X), @OfficiaPDPNig
Asali: Facebook

Jiga-jigan PDP na komawa APC a Abia

Jaridar Leadership ta ce shugaban na PDP daga 2010 zuwa 2015 ya shiga APC ne bayan wasu manyan tsofaffin 'yan PDP, ciki har da tsohon kakakin majalisar dokokin jihar, Chinedum Orji, sun koma jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Jagora a APC ya tube Ganduje, ya bayyana masu taimakon jam'iyya da gaske

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shigar Sanata Emma Nwaka zuwa APC ya zama abin mamaki a tsakanin magoya bayansa da kuma abokan hamayyarsa na siyasa, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Komawarsa APC ta bayyana ne ta hanyar wani hoto da ya yaɗu sosai a shafukan sada zumunta, wanda ya nuna shi yana karɓar katin jam’iyyar daga hannun shugaban APC na mazaɓar Oguduasa, Sampson Achi Ndukwe.

Hoton da aka yaɗa ya kuma nuna wasu manyan shugabannin jam’iyyar APC, ciki har da Udochi Okorie, shugaban APC na karamar hukumar Isuikwuato, da wasu fitattun jiga-jigan jam’iyyar.

Wannan lamari ya tabbatar da karɓarsa a matsayin sabon ɗan jam’iyyar APC bayan yin murabus ɗinsa daga PDP.

Nwaka ya yi takarar gwamna a PDP

Sanata Emma Nwaka, wanda ya wakilci Abia ta Arewa a majalisar tarayya a lokacin jamhuriya ta uku ya taɓa kasancewa ɗaya daga cikin fitattun shugabannin PDP a jihar Abia.

A shekarar 2023, ya tsaya takarar gwamna a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar PDP amma bai samu nasara ba.

Kara karanta wannan

Ganduje ya yi wa Kwankwaso shagube, ya yi barazanar kwace Kano a zaben 2027

Duk da ƙoƙarin da aka yi domin jin bakinsa kan komawarsa APC, hakan ya ci tura.

An tabbatar da komawar Nwaka zuwa APC

Sai dai wata majiya mai kusanci da shi, ta tabbatar da cewa yanzu Sanata Nwaka cikakken ɗan jam’iyyar APC ne.

Majiyar ta bayyana cewa hoton da ake yaɗawa ba wanda aka haɗa ta hanyar fasahar zamani ta AI ba ne.

"Hoton ba na AI ba ne. Idan lokaci ya yi, Sanata Nwaka zai yi magana kai tsaye da jama’a domin bayyana dalilansa na wannan babban sauyin da ya yi a siyasance."

- Wata majiya

Shigarsa APC tana zuwa ne a lokacin da wasu tsofaffin manyan 'yan PDP daga jihar suka canja sheƙa zuwa APC, wanda hakan ke nuna alamun samun sauye-sauyen siyasa a Abia.

Gwamnan Delta ya musanta batun barin PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori ya yi magana kan jita-jitar cewa yana shirin ficewa daga PDP domin komawa APC.

Kara karanta wannan

LND: Ana shirin kafa sabuwar jam'iyya domin buga APC da kasa a 2027

Gwamna Sheriff Oborevwori ya bayyana cewa babu ƙamshin gaskiya a jita-jitar, kuma bai da wani dalili da zai sanya ya fice daga PDP zuwa APC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng