'Dan Majalisar NNPP, Ya Fadi Abin da Ganduje Ya Shiryawa Jam'iyyar APC a 2027

'Dan Majalisar NNPP, Ya Fadi Abin da Ganduje Ya Shiryawa Jam'iyyar APC a 2027

  • Hon. AbdulMumin Jibrin Kofa ya ce adawa da tafiyar Kwankwasiyya ce ke jawo rigingimu a siyasar jam'iyyar APC a jihar Kano
  • Hon. Kofa, wanda ke wakiltar kananan hukumomin Kiru da Bebeji a inuwar NNPP ya ce akwai cakwakiya a siyasar Ganduje
  • Ya kara da cewa APC da Abdullahi Umar Ganduje ba za su iya tabuka komai wajen jagorancin siyasar Kano ba a yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Dan Majalisar majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Kiru da Bebeji, Hon. AbdulMumin Jibrin Kofa ya bayyana cewa sun shiryawa zabe mai zuwa.

Hon. Kofa ya ce Shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ne zai fitar wa da jam'iyyar dan takarar, duba da irin rikice-rikicen da ake fama da shi.

Kara karanta wannan

Jagora a APC ya tube Ganduje, ya bayyana masu taimakon jam'iyya da gaske

Kwankwaso
Kusa a NNPP ya ce akwai matsala a APC Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso/Abdullahi Ganduje/Hon. AbdulMumin Jibrin Kofa PhD
Asali: Facebook

2027, APC ta Ganduje ce a Kano Inji Kofa

A wani bidiyo da Freedom rediyo ta wallafa a shafinta na Fcaebook, Dan Majalisar ya bayyana cewa ko ana so, ko ba so, Abdullahi Ganduje ne APC a Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai ya na ganin jam'iyyar ba za ta yi wani tasirin kirki a jihar ba, ganin cewa wanda ake adawa da shi ya fi karfin APC da Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Hon. AbdulMumin Jibrin Kofa ya bayyana cewa jiga-jigan APC a Kano suna sane da rigingimun cikin gida da ya hana ta ci gaba a jihar Kano.

Ya kara da cewa;

"Za ka ji manyansu su na maganganu kamar babu rigima a jam'iyyar. Za ka maganar neman gwamna, ban san gaibu ba, Allah na tuba Ka gafarce ni, amma je ka rubuta, Ganduje ne zai fitar masu da dan takara, duk da dai za mu kada dan takarar ko ya fitar.

Kara karanta wannan

Dan Bilki Kwamanda: Abba ya hana ni zuwa aikin hajji duk da taimakon Kashim Shettima

Kofa ya zargi wasu daga cikin manyan APC da hada hannu wajen rashin nasarar takarar dan gidan Abdullahi Umar Ganduje a zaben da ya gabata na 2023.

Kofa: Dalilin rabuwar kai a APC

Dan majalisar na NNPP ya bayyana cewa rigingimun APC a Kano sun ki karewa ne saboda adawa da ake yi da Madugun tafiyar Kwankwasiyyya, Rabi'u Musa Kwankwaso da Gwamnan Kano.

"Abu daya ne kawai ya ke hada kan 'yan APC a Kano, Wallahi Tallahi kansu ba daya ba ne, kansu a rarrabe ya ke, rigima, yaki su ke yi da junansu.'
Abu daya ne kawai, gaba da Kwankwaso da Kwanwasiyya, gaba da Abba da gwamnatin Kano. Shikenan in ka dauke wannan, babu wani abu. To matsalar a nan shi ne, Kwankwaso ya fi karfinsu, Abba ya fi karfinsu, gwamnatin Kano ta na nan.'

Ya zargi yan APC da Abdullahi Umar Ganduje da yi wa juna tsafe-tsafe da munafurci irin na siyasa, inda ya ce rikiccin jam'iyyar ba za ta daidaitu ba.

Kara karanta wannan

Ganduje ya yi wa Kwankwaso shagube, ya yi barazanar kwace Kano a zaben 2027

Jagoran APC ya soki Abdullahi Ganduje

A wani labarin, mun ruwaito yadda kusa a siyasar APC reshen Kano, AbdulMajid Almustapha Kwamanda ya zargi Shugaban jam'iyyar na kasa, Abdullahi Ganduje da rikita jam'iyyar.

Kwamanda ya ce Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya kware a manakisar siyasa, shi ne abin da ya sa shi da mukarrabansa ke gudun a gansu da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.