Jerin Gwammonin PDP 3 da Ake Tunanin Za Su Iya Komawa Jam'iyyar APC

Jerin Gwammonin PDP 3 da Ake Tunanin Za Su Iya Komawa Jam'iyyar APC

Alamu masu ƙarfi da tushe sun nuna cewa wasu gwamnoni da suka hau karagar mulki ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP na iya sauya sheƙa zuwa APC mai mulkin ƙasa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ana ganin dai wasu daga cikin gwamnonin PDP na iya watsar da jam'iyyar su koma APC a wani ɓangare na shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027.

Gwamnonin Delta, Enugu da Filato.
Ana raɗe-raɗin wasu gwamnoni na iya barin PDP zuwa APC gabanin zaɓen 2027 Hoto: Caleb Mutfwang, Peter Mbah, Sheriff Oborevwori
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa rahoton cewa yunƙurin gwamnonin na barin PDP ba zai rasa nasaba da rigingimun cikin gida da suka dabaibaye jam'iyyar ba.

Wasu gwamnonin PDP na shirin shiga APC?

Wata majiya ta bayyana cewa wasu daga cikin gwamnonin da ake ganin mai yiwuwa za su sauya sheƙa sun fara ziyarar shugaban kasa Bola Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar majiyar, shugaban ƙungiyar gwamnonin APC kuma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma na taka muhimmiyar rawa wajen zawarcin gwamnonin PDP.

Kara karanta wannan

'Mun gano shi': Shugabannin PDP sun tabbatar gwamna zai koma APC, sun jero dalilai

A wannan babin, Legit Hausa ta tattaro maku jerin gwamnoni uku na PDP da ake zargin za su iya komawa APC saboda wasu dalilai, sai dai wasu daga ciki sun musanta.

1. Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang

Gwamnan Filato da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya na cikin gwamnonin PDP da ake raɗe-raɗin za su iya tsallakawa zuwa APC gabanin zaɓen 2027.

Caleb Mutfwang yana cikin ƴan sahun farko da suka kai wa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ziyara a gidansa da ke Legas, inda ya tafi hutun karshen shekara.

Bayan ganawa da Tinubu, Gwamna Mutfwang ya shaidawa manema labarai cewa zai marawa gwamnatin tarayya baya 100 bisa 100.

Hakan ya ƙara rura wutar zargin da ake masa cewa yana shirin jefar da PDP ya koma APC mai mulkin Najeriya.

Gwamna Mutfwang ya fito ya ƙaryata labarin zai koma APC, yana mai cewa wasu bara gurbi ne suka kirkiro jita-jitar da nufin haɗa shi faɗa da PDP.

Kara karanta wannan

'Ko a jikinmu': Gwamnan APC kan hadakar jam'iyyun adawa, ya fadi dabarbarun da za su yi

Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama'a na gwamnan Filato, Gyang Bere ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a Facebook, ya ce Mutfwang na nan daram a PDP.

2. Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori

Kalaman da gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori ya yi a wurin buɗe taron karawa juna sani na sadarwa karo na biyar ya jawo aka fara tunanin yana shirin komawa APC.

A jawabin da ya yi ta bakin kwammishinan yaɗa labarai, Ifeanyi Osuoza, gwamnan ya buƙaci mutanen Delta su marawa shugaba Bola Tinubu baya.

A cewar Gwamna Oborevwori, zai goyi bayan Tinubu ya cimma ajendarsa ta sabunta fata, sannan ya ce idan shugaban ƙasa ya gaza to shi ma ya gaza.

Haka nan kuma a makon jiya, jagororin PDP a Delta karkashin wata ƙungiya sun buƙaci mai girma gwamna ya fito ya wanke kansa daga raɗe-raɗin sauya-sheka.

Ƙungiyar ta ce ta samu labarin cewa Gwamna Oborevwori na shirin komawa jam'iyyar APC domin neman tazarce a babban zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Abin da ya hana gwamnoni taimakon Malam El Rufai lokacin da aka naɗa shi minista

Ta aika wasiƙa ga mai girma gwamnan inda ta buƙaci ya fito ya wanke kansa kan wannan jita-jitar duba da yadda yake ɗasawa da Shugaba Tinubu.

Jita-jitar ta nuna cewa gwamnan ya aika da wakilai zuwa wajen shugaban kasa Bola Tinubu don neman damar shiga jam’iyyar APC.

Sai dai a wata sanarwa da kakakin gwamnan jihar Delta, Sir Festus Ahon ranar Litinin, 6 ga watan Janairu, ya musanta jita-jitar da ke yawo cewa Oborevwori na shirin shiga APC.

A rahoton Daily Trust, Sir Festus ya ce:

“Gwamna Oborevwori ya samu karbuwa a wurin al'ummar Delta masu kishin kasa, don haka babu dalilin da zai sa ya bar jam'iyyar PDP."

3. Gwamnan Enugu, Peter Mbah

A karshen makon da ya gabata ne shugaba Tinubu ya yabawa gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, kan salon shugabancinsa da kokarin kawo ci gaba.

Tinubu ya yabi gwamnan ne da ya kai ziyara ta farko a jihar Enugu, inda ya kaddamar da ayyuka da dama da Gwamna Mbah ya kammala.

Kara karanta wannan

Wani gwamnan PDP zai sauya sheka zuwa jam'iyyar APC? Gwamnati ta fito da bayani

Gayyatar Tinubu zuwa kaddamar da ayyuka na ɗaya daga cikin dalilan da suka sa aka fara alaƙanta Peter Mbah da jam'iyyar APC.

Rahotanni sun nuna cewa Gwamna Mbah na da kyakkyawar alaƙa da Bola Tinubu, lamarin da ya ƙara rura wutar jita-jitar zai iya komawa APC gabanin 2027.

Sai dai har kawo yanzu gwamnan bai ce komai ba game da wannan jita-jita da ake yaɗawa.

Damagum ya gargaɗi masu rura rikicin PDP

A wani rahoton, kun ji cewa muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa, Umar Damagum ya gargaɗi masu amfani da kafafen sada zumunta wajen rura wutar rikicin jam'iyyar.

Ambasada Damagum ya ce wasu na yaɗa karya domin kara rikita babbar jam'iyyar adawa, ya buƙaci ƴan PDP su dawo cikin hayyacinsu kana su haɗa kansu wuri ɗaya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262