El-Rufai, Shekarau da 'Yan Siyasan da za Su iya Yakar APC da Tinubu a 2027
Yan siyasar Najeriya musamman daga Arewa na shirin kafa tafiyar siyasa domin buga APC a kasa a zaben shekarar 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja -Wasu 'yan siyasa sun fara shirin tunkarar zaben 2027 domin karawa da shugaban kasa Bola Tinubu da kawar da jam'iyyar APC daga madafun iko
Tsofaffin gwamnoni, Nasir El-Rufa'i da Ibrahim Shekarau da tsohon shugaba a APC, Salihu Lukman na cikin 'yan siyasar da suke yukurin kafa sabuwar tafiya.
A wannan rahoton, mun tattaro muku bayanai na musamman kan shirye shiryen da 'yan siyasar suke da yadda lamarin da suke kullawa zai iya shafar APC ko akasin haka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haduwar El-Rufa'ai da Hamza Al-Mustapha
A ranar Talata, wasu fitattun 'yan siyasa sun gana da shugabannin jam'iyyar SDP a babban birnin tarayya Abuja, domin tattaunawa kan makomar siyasar Najeriya a 2027.
Daily Trust ta rahoto cewa wadanda suka halarci taron sun hada da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai; tsohon dan takarar shugaban kasa, Manjo Hamza Al-Mustapha.
Haka zalika akwai jigo a jam'iyyar PDP kuma abokin siyasar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, Segun Showunmi.
Tasirin taron ga makomar siyasar 2027
Ana hasashen an yi taron ne domin tsara dabarun hadin gwiwa da nufin fitar da jam'iyyar APC mai mulki a zaben 2027, tare da samar da karfi ga jam'iyyun adawa.
Wannan taro ya zo ne kwanaki biyu bayan da El-Rufai ya musanta rade-radin cewa yana shirin ficewa daga APC zuwa jam'iyyar adawa.
A bangare guda, Segun Showunmi ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa taron ya kasance mai muhimmanci, inda ya ce:
"An kira taron ne domin duba halin da ake ciki game da rawar da jam'iyyun adawa ke takawa a Najeriya."
Duk da har zuwa yanzu, ba a bayyana cikakken bayanin taron ba, ana ganinsa a matsayin wani muhimmin mataki na tsara makomar siyasar Najeriya, musamman game da zaben 2027.
Tattaunawar samar da tafiyar siyasa
Vanguard ta rahoto cewa tsohon shugaba a APC, Salihu Lukman ya dade yana kira ga 'yan siyasa da su hada kai domin tunkarar APC a zaben 2027.
A yayin bikin sabuwar shekara, Legit ta rahoto cewa Salihu Lkuman ya ce tafiya ta yi nisa wajen kokarin samar da kungiya da za ta shiga siyasa da gaske.
"Shugabannin jam'iyyun adawa, ciki har da wasu da suka fusata daga APC, sun fara tattaunawa domin samar da sabon dandalin siyasa kafin zaɓen 2027."
- Salihu Lukman
Ya jaddada cewa dole ne a samar da jam'iyya mai aiki yadda ya kamata wadda za ta mutunta dokokinta, domin samun nasarar kawar da APC da shugaba Tinubu a zaɓen mai zuwa.
Lukman ya ja hankalin 'yan Najeriya
Lukman ya yi kira ga 'yan Najeriya da su tashi tsaye domin tabbatar da cewa kawar da APC da shugaba Tinubu a 2027 ya tabbata.
Idan suka kawar da APC, Lukman ya ce dole su tabbatar da zaɓen shugabanni na gaskiya masu bin dimokuradiyya, ba masu mulkin kama-karya ba.
A karkashin haka ne ma yake cewa dole tafiyarsu ta bambanta da salon APC, PDP, LP, NNPP da sauran jam'iyyun da ake da su a yanzu.
Kalubalen da ke gaban tafiyar Lukman
Duk da cewa an fara tattaunawa tsakanin shugabannin jam'iyyun adawa, Lukman ya nuna damuwa kan yadda yawancin 'yan siyasa ke da ra'ayin neman mulki ta kowace hanya.
A karkashin haka ya ce yana da muhimmanci a canza wannan tunanin domin samun nasarar samar da sabuwar tafiya.
Tafiyar Lukman za ta kifar da APC?
Kasancewar har yanzu Lukman bai bayyana wadanda za su yi tafiyar tare ba, da wahala a fahimci hakikanin inda suka dosa.
Duk da haka wasu na hasashen cewa tafiyar ba lallai ta yi tasiri ba musamman ganin yadda ake ganin ba hadaka za su yi da manyan jam'iyyun adawa kamar PDP da LP ko NNPP ba.
Kungiyar Shekarau za ta fada siyasa
Kungiyar dattawan Arewa ta LND ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau, na ƙoƙarin samar da sabuwar jam’iyya wadda za ta iya yin gasa da APC a zaɓen 2027.
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa kungiyar ta yi tarurruka daban-daban a baya kafin ta rikida ta sauya zuwa siyasa.
LND: Dalilin komawar tafiyar Shekarau siyasa
Wani daga cikin 'yan kungiyar ya bayyana cewa yunkurin kirkirar jam’iyyar ya samo asali ne daga gazawar APC wajen cika alkawuranta ga ‘yan Najeriya.
A bisa dukkan alamu tafiyar shekarau na shirin samar da jam’iyyr da za ta yi tsayayyiyar adawa ga APC a zaben 2027.
Duk da cewa kungiyar ta nuna cewa bata gamsu da APC da PDP ba, ana hasashen za ta iya haduwa da wasu jam’iyyun adawa domin kara karfi.
Kalubale ga tafiyar siyasar Shekarau
Duk da yunkurin kungiyar Shekarau na komawa siyasa, akwai kalubale na tabbatar da samun karɓuwa wajen ‘yan Najeriya.
Wasu masu sharhi kan siyasa suna ganin cewa yawan jam’iyyun adawa na iya rage tasirin kowace sabuwar jam’iyya, musamman idan ba a yi mata tsarin da ya dace ba.
Kungiyar za ta iya fuskantar matsin lamba daga wasu ‘yan siyasa waɗanda ke ganin cewa samar da sabuwar jam’iyya ba zai sauya komai ba a siyasar Najeriya.
Tafiyar shekarau za ta zama barazana ga APC?
Ana ganin cewa yunkurin sabuwar jam’iyyar zai iya zama babbar barazana ga APC idan aka samu nasarar jawo manyan ‘yan siyasa cikinta.
Abin da zai kara tabbatar da hasashen shi ne yadda wasu 'yan Najeriya ke kuka da salon mulkin APC duk da cewa gwamnatin tarayya ta ce a kan daidai take tafiya.
A ƙarshe, yunkurin kungiyar Shekarau na kirkirar sabuwar jam’iyya ya fara jan hankalin jama’a da kuma sanya al’umma cikin tunani kan makomar siyasa a Najeriya a 2027.
Legit ta tattauna da dan PDP
Wani matashi dan jam'iyyar PDP, Muhammad Sa'idu ya bayyana cewa ya kamata masu kokarin kafa tafiyar siyasa su marawa PDP baya.
"PDP ita ce babbar jam'iyyar adawa, kamata ya yi su shigo cikinta maimakon warewa gefe su kafa wata tafiya"
- Muhammad Sa'idu
Matashin ya ce idan suka rarrabu a jam'iyyu, hakan zai kara karfi ga APC, amma idan suka hada karfi za su iya kawo sauyi a 2027.
Sheikh Gumi ya ba Tinubu shawara
A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi kira ga Bola Tinubu kan tsaro da ake fama da 'yan bindiga musamman a Arewa.
Malamin ya yabawa shugaban kasa kan kirkiro ma'aikatar dabbobi ta kasa inda ya ce akwai bukatar amfani da ma'aikatar wajen magance matsalar tsaro.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng