An Dauko Hanyar Hada kan Kwankwaso, Ganduje, Shekarau da Sauran Manyan Kano
- Murtala Sule Garo ya bayyana cewa rashin jituwa tsakanin tsofaffin gwamnonin Kano, Kwankwaso, Shekarau da Ganduje, yana hana jihar ci gaba
- Tsohon mataimakin dan takarar gwamnan ya yi kira ga manyan jagororin da su manta da banbancin siyasa su yi aiki tare domin amfanin jihar Kano
- Haka zalika Murtala Garo ya yabawa Majalisar Dokokin Jihar Kano kan hadin kan da suka nuna, tare da neman a ci gaba da hakan domin cigaban jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Tsohon dan takarar mataimakin gwamna a APC a shekarar 2023, Murtala Sule Garo ya yi kira domin samun hadin kan manyan 'yan siyasar Kano.
Murtala Sule Garo ya bayyana cewa rikicin siyasa da ke tsakanin tsofaffin gwamnonin Kano, Kwankwaso, Shekarau da Ganduje, yana hana jihar samun ci gaba.
Daily Trust ta wallafa cewa Garo ya ce lokaci ya yi da tsofaffin gwamnonin za su manta da bambance-bambancen siyasa su yi aiki tare domin ciyar da jihar Kano gaba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa idan ana son ganin jihar ta samu ci gaba mai dorewa, dole ne a samar da hadin kai tsakanin shugabanni da sauran masu ruwa da tsaki.
Muhimmancin hadin kan shugabannin Kano
Murtala Garo ya nuna takaici kan yadda tsofaffin gwamnonin jihohin da ba su kai Kano ba, irinsu Zamfara, suke haduwa su tattauna batutuwan da suka shafi jiharsu, amma Kano ta gagara.
“Abin takaici ne a ce tsofaffin gwamnonin Kano ba su cika haduwa domin tattauna matsalolin jihar ba,
'Alhali wasu jihohi da ba su kai Kano ba suna yin haka domin ciyar da jiharsu gaba.
"Wannan yana kawo koma baya ga cigaban jihar Kano.”
- Murtala Sule Garo
Haka zalika ya kara da cewa,
“Ina kira ga tsofaffin gwamnoninmu da su manta da sabanin da ke tsakaninsu, su yi aiki tare domin cigaban Kano.
"Hadin kai shi ne kashin bayan samun ci gaba mai dorewa, kuma ya kamata wannan ya zama abin da suka fifita”
Yabo ga majalisar dokokin Kano
A wani bangare na jawabinsa, Garo ya yaba wa ‘yan Majalisar Dokokin Jihar Kano kan hadin kan da suka nuna, ya bayyana hakan a matsayin abin koyi ga sauran shugabanni.
“Ina rokon sauran ‘yan siyasa su daina duk wani abu da zai kawo baraka a tsakanin ‘yan majalisa.
Wannan hadin kai da suka nuna shi ne asalin abin da ke kawo ci gaba. Idan aka ci gaba da haka, babu shakka Kano za ta ga ci gaba.”
Ya kuma bayyana cewa idan shugabannin siyasa za su koyi darasi daga wannan hadin kan, za a iya samar da tsari mai kyau da zai ciyar da jihar gaba.
A karshe, Garo ya yi kira ga dukkan shugabannin siyasa da su mayar da hankali kan abin da zai kawo cigaban jihar Kano, maimakon rikice-rikicen da ba su da amfani.
Abba ya bukaci rage kudin aikin Hajji
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi kira na musamman ga shugaba Bola Tinubu kan Hajjin bana.
Abba Kabir Yusuf ya ce ya kamata gwamnatin tarayya ta rage kudin aikin Hajjin shekarar 2025 lura da matsin tattalin arziki da ake fuskanta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng