Zargin Barazana: Atiku Ya Shiga Fadan Peter Obi da Tinubu, Ya ba da Shawara

Zargin Barazana: Atiku Ya Shiga Fadan Peter Obi da Tinubu, Ya ba da Shawara

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya shiga rigima tsakanin gwamnatin Bola Tinubu da Peter Obi
  • Atiku ya ce maganganun kakakin jam'iyyar APC, Felix Morka a kan Peter Obi, sun nuna wata alama ta rashin yarda da 'yancin masu adawa
  • Ya ce kalaman da suka nuna Obi ya "ketare iyaka" sun bayyana rashin girmamawa ga dimukradiyya da muhimmancin muhawara mai amfani
  • Wannan na zuwa ne bayan Peter Obi ya zargi gwamnatin ta yi masa barazana kan sukar manufofinta da ke nuna alamar kama-karya a siyasa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya magantu kan zargin da Peter Obi ya yi kan gwamnatin Bola Tinubu.

Atiku Abubakar ya ce abin takaici ne maganganun da Felix Morka, kakakin APC, ya yi wa Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa a LP.

Kara karanta wannan

Shugaban FIRS zai ajiye kujerarsa domin neman gwamna? Gaskiya ta fito

Atiku ya caccaki APC kan barazana ga Obi
Atiku Abubakar ya dura kan gwamnatin Bola Tinubu da APC kan barazana ga Peter Obi. Hoto: Atiku Abubakar, Peter Obi, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Atiku ya soki gwamnatin Tinubu kan 'yan adawa

Atiku ya bayyana haka ne a yau Talata 7 ga watan Janairun 2025 a shafinsa na X, ya ce hakan rashin girmama dimukraɗiyya ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon mataimakin shugaban kasa ya ce barazanar da aka yi wa Obi, tare da tsare da wasu masu sukar gwamnati ya nuna yadda hakkin 'yan adawa ke ƙara lalacewa.

Ya ce kalaman da aka ce Obi ya "ketare iyaka" suna nuna tsanani da rashin amincewa da tsarin dimukradiyya a cikin Najeriya mai 'yancin faɗin albarkacin baki

Peter Obi: Atiku ya caccaki kakakin APC

"Dimukradiyya tana zama mai amfani ne idan aka saurari ra'ayoyi daban-daban, kalaman da Morka ya yi sun nuna rashin fahimta da mahimmancin wannan tsari."
"Maganganun da APC ta yi sun ƙunshi barazana da ke nuna cewa Obi ya kasance cikin hatsari, kuma hakan ya dace a bayyana makasudinsu."
"Rashin girmamawa da APC ta yi wa Obi ta hanyar kwatanta shi da cewa ya wuce ka'ida ba abu ne da za a amince da shi ba."

Kara karanta wannan

'Na san za a zage ni': Tinubu ya fadi shirin da yake yi wa Najeriya

- Cewar sanarwar

Shawarar da Atiku ya ba gwamnatin Tinubu

Atiku ya kalaman Morka suna iya kawo rarrabuwar kai da tashin hankali a cikin al'umma, domin ba su ƙarfafa tattaunawar siyasa mai ma'ana.

Ya ce gwamnati ta cancanci yin gyara ta hanyar ba wa masu sukarta damar tattaunawa mai fa'ida, ba tare da barazana ko tsoratarwa ba.

Har ila yau, Atiku ya ce wajibi ne APC ta nemi gafarar Peter Obi da 'yan Najeriya baki ɗaya kan waɗannan maganganun da ba su dace ba.

Ya ce yin amfani da kalmomi masu kyau a muhawara tsakanin jam'iyyu zai iya kawo ci gaba ga al'umma, maimakon yin amfani da barazana ko wulakanci.

Obi ya zargi Tinubu da yi masa barazana

Kun ji cewa jigo a jam'iyyar adawa ta LP, Peter Obi ya faɗi halin da ya tsinci kansa a ciki saboda sukar gwamnatin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

'Abin da ya sa Yar'Adua soke siyar da matatar mai ga Dangote da Obasanjo ya roka'

Dan takarar shugaban ƙasan na zaɓen 2023 ya bayyana cewa ana yi wa rayuwarsa barazana saboda fitowa ya faɗi gaskiya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.