Kano: Ƴan Kwankwasiyya Sun Tashi da Nauyi, Gwamna Abba Ya ba Su Miliyoyin Naira
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sha alwashin faɗaɗa ayyukan kungiyar ƴan midiya na Kwankwasiyya saboda gudummuwar da suke ba gwamnatinsa
- Abba ya ba ƴan kundgiyar tallafin Naira miliyan 30 domin ƙara masu kwarin guiwa wajen wayar da kan jama'a a jihar Kano
- Ya ce zai zauna da shugabannin ƙungiyar domin tattaunawa kan wasu ayyukan ba da tallafi da gwamnatinsa za ta yi a nan gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin fadada ayyukan ƙungiyar ƴan midiya na Kwankwasiyya saboda gudummuwar da suke bayarwa.
Gwamna Abba ya kuma bai wa ƴan kungiyar tallafin Naira miliyan 30 a wani mataki na yaba masu bisa jajircewa da kuma yaɗa manufofin gwamnatinsa.
Abba Kabir ya bayyana hakan ne a wurin wani taron rabon tallafi wanda ƙungiyar ƴan midiyar Kwankwasiyya ta shirya a ɗakin taron gidan gwamnatin Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook yau Litinin.
Gwamma Abba zai faɗaɗa ayyukan Kwankwasiyya
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Yusuf ya jaddada rawar da kungiyar mai suna, 'Kwankwasiyya Media Forum' ke takawa wajen kusantar da gwamnati ga al’umma.
A cewarsa, suna taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da cewa jama’a suna samun cikakken bayani kan ayyukan ci gaban da gwamnatinsa ke aiwatarwa.
Gwamnan ya ce duk ƙanƙantar tallafi yana iya kawo farin ciki da ƙwarin gwiwa ga waɗanda suka amfana.
Ya bayyana taron bada tallafin da kungiyar ta shirya a matsayin mai cike da tarihi, wanda ya zo daidai da cikarsa shekaru 62 a duniya kuma shi ne taro na farko da ya halarta a 2025.
Gwamnan Kano ba kungiyar kyautar N30m
Bugu da ƙari, Gwamna Abba ya sanar da bayar da gudunmawar Naira miliyan 30 ga ƴan ƙungiyar domin karfafa ayyukan wayar da kan jama’a da kuma yada manufofin gwamnatinsa.
Gwamnan ya jinjinawa ƴan kungiyar bisa yadda suke gudanar da harkokinsu cikin kwarewa, musamman wajen mu’amala da jam’iyyun adawa.
Ya bukaci su ci gaba da kasancewa masu adalci da ladabi a duk al'amuransu, yana mai cewa irin wannan hali n iya jawo hankalin masu sukar NNPP su amince da manufofinta.
Shugabannin kungiyar sun sha yabo
Abba Kabir ya kuma yabawa shugaban ƙungiyar ƴan midiya na Kwankwasiyya, Alhaji Nagoda, da sauran jagorori kamar Murtala Zawai, Nura Bakwankwashe, da Ali Gyara Hausawa.
"Gwamna Abba Kabir ya yaba masu bisa jajircewa wajen tallafawa kafofin watsa labarai da kuma wayar da kan jama’a game da ayyukan gwamnatinsa a Kano," in ji sanarwar.
Har ila yau. gwamnan ya tabbatar musu da cewa za su ci gaba da yin aiki tare, sannan ya yi alkawarin ganawa da shugabannin ƙungiyar domin tattaunawa.
Tun da farko, Alhaji Nagoda, ya bayyana cewa sun tara Naira miliyan 11 daga ƴan jam’iyyar NNPP, kwamishinoni, da wasu masu ruwa da tsaki domin faɗaɗa shirinsu.
Abba Kabir ya naɗa sababbin hadimai 5
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙara yin sababbin naɗe-naɗe guda biyar a gwamnatinsa.
Kakakin gwamna, Sanusi Dawakin Tofa ya ce Abba ya naɗa masu ba shi shawara na musamman guda biyar kuma za su karbi rantsuwar kama aiki ranar Litinin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng