2027: Ana Zargin Wasu Gwamnonin PDP da Shirin Sauya Sheka zuwa APC

2027: Ana Zargin Wasu Gwamnonin PDP da Shirin Sauya Sheka zuwa APC

  • Rahotanni sun nuna cewa an fara rade radin gwamnonin PDP na shirin barin jam’iyyarsu zuwa APC saboda rikice-rikice da ke addabar jam’iyyar
  • Ana zargin cewa wasu daga cikin gwamnonin PDP sun fara ziyartar shugaba Bola Tinubu a Legas domin tattaunawa kan siyasa da wasu lamura
  • Wata kungiya a jihar Delta ta bukaci Gwamna Sheriff Oborevwori ya fitar da sanarwa game da jita-jitar cewa yana shirin barin PDP zuwa APC

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rahotanni sun nuna yiwuwar wasu gwamnonin jam’iyyar PDP za su sauya sheka zuwa APC kafin babban zaben shekarar 2027.

Wata majiya ta bayyana cewa rikice-rikice a matakan jam’iyyar PDP, musamman a kwamitin ayyuka na kasa (NWC) da wasu jihohi, na daga cikin dalilan sauyin sheka da ake tsammani.

Kara karanta wannan

Ganduje ya yi wa Kwankwaso shagube, ya yi barazanar kwace Kano a zaben 2027

Jam'iyyar PDP
Ana zargin wasu gwamnonin PDP da shirin komawa APC. Hoto: Senator Bala Abdulkadir Mohammed
Asali: Twitter

Rahoton jaridar Vanguard ya bayyana cewa, wasu gwamnonin PDP sun riga sun fara ziyartar Shugaba Bola Tinubu domin tattaunawa da kuma neman goyon baya kan wasu batutuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa gwamnonin PDP za su sauya sheka?

Majiyoyi daga jam’iyyar PDP sun tabbatar da cewa rikice-rikicen da ke addabar jam’iyyar sun zame mata babbar barazana, musamman a matakin jihohi da na kasa.

Ana ganin hakan na daya daga cikin dalilan da suka sa gwamnonin jam’iyyar ke tunanin sauya sheka zuwa jam’iyyar APC domin tabbatar da matsayin siyasar su.

Ana ganin cewa rikice-rikicen sun jefa jam’iyyar cikin yanayin rashin tabbas, musamman yayin da ake gab da fara shiri na babban zaben shekarar 2027.

Wata majiya ta kara da cewa rashin cimma matsaya kan wasu muhimman abubuwa a matakin jihohi da yankuna ya kara rura wutar rikicin.

Tinubu da gwamnonin PDP sun fara tattaunawa

Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu daga cikin gwamnonin PDP sun riga sun fara ziyartar Shugaba Bola Tinubu a gidansa da ke Bourdillon, Legas.

Kara karanta wannan

LND: Ana shirin kafa sabuwar jam'iyya domin buga APC da kasa a 2027

Ana hasashen cewa ziyarar na nufin tattaunawa kan batutuwan da suka shafi sauyin sheka, tare da neman goyon bayan shugaban kasa.

Haka zalika, wasu daga cikin gwamnonin sun gayyaci Shugaba Tinubu domin kaddamar da ayyukan raya kasa a jihohinsu.

Ana ganin cewa wannan dama ce da suke amfani da ita wajen tattaunawa kan makomar siyasar su a APC.

Kungiyar PDP a Delta ta gargadi gwamna

A jihar Delta, wata kungiyar PDP ta yi kira ga Gwamna Sheriff Oborevwori ya yi karin bayani kan rade-radin cewa yana shirin sauya sheka zuwa APC.

Kungiyar ta bayyana cewa jita-jitar ta yawaita cewa gwamnan yana tuntubar wasu manyan mukarraban shugaba Tinubu da nufin shiga jam’iyyar APC.

Sheriff Oborevwori
Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori. Hoto: Delta State Government.
Asali: Twitter

A cikin wata budaddiyar wasika da suka rubuta, kungiyar ta bayyana cewa idan gwamnan bai yi karin bayani cikin lokaci ba, za a dauki shiru nasa a matsayin tabbatar da rade-radin.

Kara karanta wannan

APC: El Rufa’i ya bayyana matsayinsa kan jita jitar sauya sheka

The Nation ta ruwaito cewa kungiyar ta ce wannan lamarin na iya haifar da rashin tabbaci a cikin jam’iyyar PDP a jihar Delta.

Shekarau na shirin kafa sabuwar jam'iyya

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Ibrahim Shekarau ya fara kokarin dawo da kungiyar NLD zuwa jam'iyyar siyasa.

Sanata Shekarau ya bayyana cewa za su mayar da kungiyar jam'iyyar siyasa domin kawo karshen mulkin APC a zaben 2027 da kafa mulkin adalci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng