APC: El Rufa’i Ya Bayyana Matsayinsa Kan Jita jitar Sauya Sheka

APC: El Rufa’i Ya Bayyana Matsayinsa Kan Jita jitar Sauya Sheka

  • Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya karyata rade-radin da ke yawo cewa ya bar jam’iyyarsa ta APC
  • El Rufa'i, wanda tsohon Ministan Abuja ne ya ce labarin kanzon kurege ne, kuma ba zai lamunci irin wannan ba
  • Ya ce zuwa yanzu ya gano wadanda ke jagorantar yada labarin bogin, kuma tuni ya ba lauyoyinsa umarni kan batun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya karyata rade-radin da ke yawo cewa ya bar jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar adawa ta PDP.

Rahotannin sun fara yaduwa ne bayan wasu kalaman El-Rufa’i da ake ganin suna sukar zargin wariyar kabilanci a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

'Duk da amaryata ‘yar shekara 14 ta nemi kashe ni da guba, ina kaunarta' inji Ango

Nasir
El Rufa'i ya karyata sauya jam'iyya Hoto: Nasir El Rufa'i
Asali: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, El-Rufa’i ya wanke kansa daga zargin komawa PDP, inda bayyana rahoton a matsayin karya tsagwaron da ba shi da tushe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma bayyana irin matakin da ya ke shirin dauka a kan masu son jawo maganganu a siyasarsa ta hanyar danganta shi da barin jam'iyya.

El Rufa'i ya gano masu yada labarin komawarsa PDP

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, El-Rufa’i ya bayyana cewa ya gano wadanda ke jagorantar yada wannan karya, inda ya zarge su da yunkurin bata sunansa tare da haddasa rudani.

Ya kuma gargadi masu yada wannan labari cewa ba zai yarda da irin wannan cin zarafi ba, yana mai kiran su da sunan masu yada farfaganda mara gaskiya da son rijiya siyasarsa.

Nasir El Rufa'i zai dauki matakin shari'a

El-Rufa’i ya sanar da cewa lauyoyinsa sun fara daukar matakin shari’a kan wadanda ke yada wannan labari na bogi domin abbatar da cewa sun fuskanci hukunci.

Kara karanta wannan

Satar waya: 'Yan sanda sun yi tara tara, an damke Shamsiyya da yaranta a Kano

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa ba zai lamunci irin wannan ba, saboda haka ne ma ya shiga daukar matakin shari'a a kan wadanda ya ke zargin su ne jagororin yada labarin.

A cikin sakonsa da ya wallafa, El Rufa'i ya ce:

"A yi watsi da wannan labarin karya game da sauya jam’iyyata. Na bai wa lauyoyina umarnin su dauki matakin doka kan wadanda ke yada wannan karyar.”

El Rufa'i ya ziyarci gidan yari

A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El Rufa'i ya ziyarci gidan yarin da ake girke tsohon Shugaban ma'aikatansa, Bashir Sa'idu bisa wasu zarge-zarge.

Ana zargin Bashir Sa'idu da almundahana a gwamnatin Nasir El Rufa'i, sai dai tsohon gwamnan bai ce uffan a amma tuhume-tuhumen da ake zargin an tafka a lokacin ya na gwamna ba.

Ziyarar ta tsohon gwamna, El-Rufai na zuwa ne bayan kama Bashir a ranar Litinin da gurfanar da shi a gaban kotun majistare da ke Rigasa, wacce ta ba da umarnin tsare shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.