‘Na San Za a Zage ni’: Tinubu Ya Fadi Shirin da Yake Yi wa Najeriya

‘Na San Za a Zage ni’: Tinubu Ya Fadi Shirin da Yake Yi wa Najeriya

  • Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa yana da gogewa da sanin yadda za a gudanar da mulki tare da kafa ingantaccen tawaga don gina ƙasa
  • Tinubu ya bayyana cewa cire tallafin mai ya zama dole don kare makomar matasa da gina ƙasar da za a yi alfahari da ita
  • Shugaban ya yi kira ga al’ummar kudu maso gabas su zama tsintsiya madaurinki ɗaya don ciyar da Najeriya gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Enugu - Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa yana da cikakken sani kan yadda ake tafiyar da mulki don gina Najeriya.

Tinubu ya ce dole ce ta sanya shi cire tallafin man fetur domin inganta rayuwar matasa da kuma gina kasa.

Tinubu ya fadi shirin da yake yi wa Najeriya
Bola Tinubu ya ce ya sani za a zage shi amma ya san yadda ake gudanar da mulki. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Tinubu ya kaddamar da ayyuka a Enugu

Tinubu ya yi wannan jawabi ne a Enugu yayin ganawarsa da masu ruwa da tsaki a wani bidiyo da shafin @PBATMediaCentre ya wallafa a X.

Kara karanta wannan

NNPP: 'Yan adawa sun gano lagon karya Tinubu, sun ce mulki zai dawo Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin wannan ziyara, wanda ita ce ta farko da ya kai jihar a hukumance, Shugaban ya ƙaddamar da ayyuka da gwamnan jihar, Peter Mbah, ya fara.

Daga cikin ayyukan da aka ƙaddamar akwai makarantu guda 30 masu fasahar zamani, cibiyoyin lafiya guda 60 da titin Airport-New Haven-Bisalla zuwa Okpara Square.

Tinubu ya ce cire tallafin mai ya zama dole don tabbatar da ci gaban ƙasa da kare makomar matasan Najeriya.

Tinubu ya fadi kwarewarsa kan mulki

“Ku duka mambobi ne na babban iyali guda mai suna Najeriya, amma kowa na zaune ne a ɗaki daban-daban a cikin gida guda, wannan gida, dole ne mu gina shi, domin biyan buƙatun yanzu da kuma na gaba.”
“Ba za ku kashe makomar al’ummar da ba su zo ba kafin a haife su ba, ka da ku lalata ƙasa kafin su zo duniya."
"Na san mutane za su yi faɗa, guna-guni, su zage ni da duk wani abu, amma na nemi wannan aiki, na san abin da ya ƙunsa, kuma ina da tabbacin zan iya kafa tawaga mai kyau don gina ƙasa.”

Kara karanta wannan

Yadda aka 'tsorata' Tinubu ya ki karbar minista a gwamnatin Yar'adua

- Bola Tinubu

Shugaban ya yi kira ga al’umma da su sauya tunani kan mummunan ra'ayi game da Najeriya inda ya ce yana alfahari da Najeriya, ya kamata kowa ya kasance mai alfahari.

Tsohon Minista daga Kano ya yabi Tinubu

Kun ji cewa tsohon Ministan Gidaje, Dr. Abdullahi Tijjani Gwarzo, ya yaba wa Bola Tinubu kan jagoranci da gyare-gyare don ci gaban Najeriya.

Gwarzo ya jinjina wa 'yan Najeriya bisa jajircewa wajen tallafa wa hangen nesa na Shugaba Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.