Tsohon ‘Dan APC Ya Bada Labarin Yadda Aka Rabawa Buhari Hankali da Takarar Tinubu
- Osita Okechukwu ya ce an kai ruwa rana a lokacin da Bola Ahmed Tinubu ya fito neman takara a APC
- Wasu sun so kwamitin John-Odigie Oyegun ya kori wasu cikin masu sha’awar takarar shugaban kasa
- Mutanen Muhammadu Buhari sun rabu biyu game da goyon bayan Bola Tinubu inji Cif Osita Okechukwu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Daya daga cikin wadanda aka kafa APC da su a Najeriya, Osita Okechukwu, ya bude shafin John-Odigie Oyegun da zaben 2023.
Osita Okechukwu ya tabo batun yadda aka zabi John-Odigie Oyegun ya zama shugaban kwamitin tantance masu neman takara.
Okechukwu: 'Takarar Tinubu ta raba kan Buhari'
Daily Trust ta rahoto ‘dan siyasar ya ce an nemi a samu rabuwar kai da aka nada John Oyegun ya yi aikin tsaida ‘dan takarar shugaban kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayanin Osita Okechukwu ya kasance kamar martani ga Babafemi Ojudu wanda ya ce ba a goyi bayan Bola Tinubu a zaben jam'iyyar APC ba.
Okechukwu wanda yana cikin wadanda ya yi aiki a gwamnatin Buhari ya tabbatar da cewa an samu rabuwar kai a fadar Muhammadu Buhari.
"Eh shakka babu an samu rabuwar kai a kan za a goyi bayan Tinubu ko kuwa
Kuma Muhammadu Buhari ya tsaya tare da mutanen da ke bayan ministan ilmi a lokacin, Malam Adamu Adamu,
Ya jawo ayar Kur’ani ya na cewa ba zai yi watsi da mutumin da ya tsaye masa dare da rana ba."
- Osita Okechukwu
Muhammadu Buhari ya ce a zabi Tinubu?
Tsohon shugaban na VOA yake cewa a karshe a kan yanke matsaya cewa a tafi filin zabe, ‘yan APC su zabi wanda suke so a ba tuta.
Cif Okechukwu ya ce an bijiro da zancen hana daya daga cikin masu neman tikitin takara saboda zargin da ake ji ya na yawo.
Inda ya yarda da Ojudu kurum shi ne kan matsayar Buhari, ya ce bai fifita kowa ba, kuma duk wanda ya nuna to shi zai samu takara.
Idan da Muhammadu Buhari ya ce a zabi Ahmad Lawan, Okechukwu ya ce da shi zai samu tikiti, amma ya kyale aka zabi Bola Tinubu.
'Yan siyasar da suka bi Bola Tinubu
Akwai shahararrun 'yan siyasar adawa da yawa da suka sauya-sheka a shekarar bara kamar yadda muka tattaro jerinsu kwanaki.
Anyim Pius Anyim yana cikin wadanda shigowarsu APC za ta iya murkusa karfin adawa domin ya nemi tikitin shugaban kasa.
Asali: Legit.ng