2023: Jigon APC ya ambaci wanda ake zargin APC za ta ba takarar Shugaban kasa

2023: Jigon APC ya ambaci wanda ake zargin APC za ta ba takarar Shugaban kasa

Osita Okechukwu ya ce Bola Tinubu zai iya samun takarar APC a zaben 2023

‘Dan siyasar ya bayyana cewa babu alkawari cewa Buhari zai ba Tinubu mulki

Okechukwu ya ba don Tinubu musulmi ba ne, da ya zama mataimakin Buhari

Daya daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar APC, Mista Osita Okechukwu, ya na ganin Asiwaju Ahmed Bola Tinubu zai iya samun tikiti a zaben 2023.

Osita Okechukwu ya bayyana cewa tsohon gwamnan na Legas ne zai iya yin dace idan APC ta zabi a fito da ‘dan takara ba tare da zaben tsaida gwani ba.

Darekta Janar na VON, Okechukwu yace wannan tunani da APC ta ke yi na fito da ‘dan takarar shugaban kasa ta hanyar yin i’itifaki zai taimaka wa jam’iyyar.

Da yake hira da Guardian, Osita Okechukwu, ya yabi shugabannin jam’iyyar a kan wannan shawarar.

“Mutum ya yi barci da idanu biyu a daren jiya bayan samun labarin jawabin sakataren mu na kasa, Sanata John Akpanudedehe, da ya ce za a fito da wanda zai yi wa APC takarar shugaban kasa ta hanyar mubaya’a a zaben 2023.”

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta yi karin bayani a kan yadda ‘Dan takarar Shugaban kasan 2023 zai fito

“Ina tunanin (Tinubu) ya na cikin manyan ‘yan takarar da za ayi la’akari da su, ganin irin gudumuwar da ya bada wajen cigaban jam’iyyarmu a zaben shekarar 2015.”

2023: Jigon APC ya ambaci wanda ake zargin APC za ta ba takarar Shugaban kasa
Tinubu da Buhari Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Okechukwu yake cewa babu wata yarjejeniya da aka yi tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da jagoran na APC, Bola Tinubu cewa za su gaji juna a shekarar 2023.

“A matsayina na tsohon ‘dan jam’iyyar CPC, ban taba jin labarin wannan yarjejeniya ba. Kuma shugaban kasa ba zai taba jefa kansa cikin wannan da kowa ba.”
“Da Asiwaju ne zai zama mataimakin shugaban kasa, amma zai aka yi tsoron Muslmai biyu su yi takara.”
“Shugabanninmu sun ce cacar Abiola/Kingibe da aka yi a shekarar 1993 ba zai yi aiki a 2015 ba. Idan Buhari da Tinubu su ka yi takara, ba za su ci ba, wannan ya kawo Yemi Osinbajo."

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng