Tinubu ya karyata labarin ‘sharrin’ da ake yi masa ana tsakiyar zaben ‘Dan takara a APC

Tinubu ya karyata labarin ‘sharrin’ da ake yi masa ana tsakiyar zaben ‘Dan takara a APC

  • Ofishin yada labaran Asiwaju Bola Ahmed Tinubu sun fitar da wata muhimiyyar sanarwa a jiya
  • Rade-radi na yawo cewa Bola Tinubu zai dauko Musulmi ne a matsayin ‘dan takarar mataimaki
  • Jigon na APC ya ce wannan labari ba gaskiya ba ne, ya nuna ba a fara maganar abokin takara ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya karyata labarin da yake yawo a halin yanzu a game da zabinsa na ‘dan takarar mataimakin shugaban Najeriya.

A wata sanarwa da ta fito wanda ta shigo hannun Legit.ng Hausa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya ce babu gaskiyar cewa zai dauko Musulmi ne a tikitinsa.

Sanarwar ta fito ne daga ofishin yakin neman zaben Bola Tinubu a ranar Talata, 7 ga watan Yuni 2022.

Taken takardar da aka fitar shi ne ayi hattara da labaran bogi, inda aka nuna maganar da ake fadawa masu tsaida ‘dan takara a APC sam ba daidai ba ne.

Kara karanta wannan

Maganar tsaida ‘dan takarar shugaban kasa ta hanyar lalama ta balbalce ana gobe zaben APC

“Mun samu labarin wani sako da yake yawo a Eagle Square a wajen tsaida ‘dan takara da sunan cewa daga wajen Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya fito.
Ana ikirarin ya samu nasara a zaben tsaida gwani, ya zama ‘dan takarar shugaban kasa, har jagoran na APC ya yarda ya dauko Musulmi a tikitinsa."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tinubu ya karyata rade-radi
Jawabin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: @Mr_JAGs
Asali: Twitter
“Wannan ba komai ba ne face karya wanda bai da tushe ko ta ina. Mu na kira ga masu zaben ‘dan takararmu da su yi watsi da wannan gaba daya”
“Wannan sako yunkuri ne na wasu miyagu na kawo rudani, su yaudari masu zaben ‘dan takara ganin cewa Bola Tinubu ya na kan samu nasara."

Ba a kai wannan gabar ba

Har ila yau, sanarwar ta nuna cewa tsohon gwamnan na Legas zai ji da maganar wanda zai zama masa mataimaki ne bayan ya lashe zaben da ake shiryawa.

Kara karanta wannan

Tashin nakiya a coci: Ana ta zaben fidda gwani, Tinubu ya tafi jihar Ondo ziyara

Jawabin ya ce ba a san Asiwaju (Tinubu) da garaje ba. Zai dauki mataki kan muhimman abubuwan da suka shafi abokin takara a lokacin da ya dace.

Ganin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Musulmi ne da ya fito daga kudu, wasu ke ganin cewa zai dauko Musulmi daga Arewa ne domin su yi takara tare a 2023.

An samu cikas kadan

Yayin da ‘Yan jam’iyya daga Kano suke kada kuri’a, sai aka ji labari an dakatar da zabe, amma yanzu abubuwa sun cigaba da tafiya yadda ya kamata a farfajiyar.

Kwamitin shirya zaben ya ji tsoron cewa akwai ‘Yan takara uku da ke dauke da ‘Ahmad’ a cikin sunayensu, hakan ta sa aka dauki mataki kafin a samu rudani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel