Kwankwaso Ya Fadi Abin da Ke Kawo Cikas a Fitar da Yan Takara, Ya Shawarci Dattawan Arewa

Kwankwaso Ya Fadi Abin da Ke Kawo Cikas a Fitar da Yan Takara, Ya Shawarci Dattawan Arewa

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda wasu jagorori ke tsoma kansu wajen fitar da 'yan takara a Arewa
  • Kwankwaso ya bayyana cewa irin wannan dabi'a tana raba kan jama'a tare da kawo cikas ga dimokuradiyya da zaɓen shugabanni marasa cancanta
  • Sanatan ya buƙaci dattawan Arewa su daina son rai wajen fitar da 'yan takara, musamman a zaɓen shugaban ƙasa na gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana kan rawar da wasu ke takawa kan fitar da yan takara.

Kwankwaso ya bayyana damuwarsa game da yadda wasu ke tsoma baki wajen zaɓen 'yan takarar shugabancin ƙasa, da sunan wakiltar Arewa.

Kwankwaso ya soki yan Arewa kan fitar da yan takara
Sanata Rabiu Kwankwaso kan tsoma baki da dattawan Arewa ke yi a fitar da yan takara. Hoto: Sanata Rabi'u Kwankwaso.
Asali: Facebook

Kwankwaso ya ba dattawan Arewa shawara

Yayin wata hira da BBC Hausa, Kwankwaso ya ce irin wannan tsoma baki na jawo matsala a dimokuradiyya tare da haifar da rarrabuwan kawunan jama'a.

Kara karanta wannan

"Tinubu na kan siraɗi": Peter Obi ya yi magana kan haɗa kai da Kwankwaso da Atiku

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso ya ce bai kamata dattawan yankin suna shiga lamarin ba wanda ke kawo tarnaki ga al'umma.

Ya buƙaci dattawan su tsame kansu daga tsoma baki, musamman idan abin zai kawo rashin adalci ko rashin daidaito a tsakanin al'umma.

“Wannan abu da suke yi na zalunci yana haifar da tarnaki a tsakanin al’umma."
"Bai kamata dattawanmu su riƙa nuna son rai wajen zaɓen ‘yan takara ba."

- Rabi'u Kwankwaso

Kwankwaso ya soki dattawan Arewa kan yan takara

Tsohon gwamnan ya bayar da misali da zaɓen 2019, inda ya ce wasu dattawa daga Arewa maso Yamma sun yi amfani da son zuciya wajen fitar da ‘yan takara.

“Yawanci suna zuwa su kitsa ƙarya, suna faɗin cewa Arewa ta amince da wannan ko wancan, amma daga ƙarshe hakan yana jawo koma-baya,"

- Cewar Kwankwaso

Kwankwaso ya ƙara jan hankali kan muhimmancin gaskiya da adalci wajen jagoranci.

Kara karanta wannan

"Jiki duk yunwa," Tsohon shugaban majalisa ya fadi illar barin Arewa talauci

An yi wa Kwankwaso rubdugu kan Atiku

Kun ji cewa kalaman da Rabiu Kwankwaso ya yi cewa Atiku Abubakar maƙaryaci ne sun harzuƙa matasa masu goyon bayan Wazirin Adamawa.

Kungiyar NYFA ta gargaɗi jagoran NNPP na ƙasa kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Rabiu Kwankwaso ya daina taɓa mutuncin Atiku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.