2027: Shugaban NNPP na Kano Ya Jawo Wa Kansa Magana Mai Zafi kan Tazarcen Tinubu
- Kungiyar magoya bayan APC a Arewa ta Tsakiya ta bayyana cewa babu wani sihiri ko shiri da zai hana Bola Tinubu tazarce a 2027
- Shugaban kungiyar, Alhaji Saleh Zazzaga ne ya faɗi haka da yake martani ga jam'iyyar NNPP ta reshen jihar Kano ranar Juma'a
- Ya ce kyawawan tsare-tsaren da Bola Tinubu ya aiwatar a gwamnatinsa kaɗai za su sa ƴan Najeriya su ƙara zaɓensa karo na biyu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Kungiyar APC a Arewa ta Tsakiya ta ce babu wani sihiri ko ƙulumboto da zai hana tazarcen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a 2027.
Shugaban ƙungiyar, Alhaji Saleh Zazzaga ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a, 3 ga watan Janairu, 2025 a Abuja.
Saleh Zazzaga ya ce manufofin Shugaba Tinubu za su ɗaga ƙimar Najeriya, sannan su ƙara masa farin jini a wurin ƴan ƙasa, Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban NNPP na Kano ya tayar da ƙura
Ya yi wannan furuci ne da yake martani ga shugaban NNPP na jihar Kano, Hashimu Dungurawa, wanda ya shawarci Tinubu ta fara shirin barin Aso Rock a 2027.
Idan za ku iya tunawa shugaban NNPP ya yi ikirarin cewa ƴan Najeriya za su yi watsi da Bola Tinubu a zaɓen 2027 saboda tsare-tsarensa da suka ƙaro talauci.
A rahoton Punch, Hashimu Dungurawa ya ce:
"Duba da waɗannan matsaloli da wasu masu ɗumbin yawa da gwamnatin APC ta kawo, ina ganin lokaci kawai mu ke jira amma zamu tabbatar da Tinubu ya bar mulki, Kwankwaso ya ɗare."
Babu abin da zai hana tazarcen Tinubu
Da yake mayar da martani ga shugaban NNPP, Saleh Zazzaga ya ce babu tantama Bola Tinubu zai yi tazarce a inuwar jam'iyyar APC a 2027.
"Babu wani sihiri da zai sa Tinubu ya fadi zaben shugaban kasa a 2027, haka nan ba zai yiwu gwamnatin APC karkashin Shugaba Tinubu ta gaza zarcewa wa'adi na biyu ba."
"Kuma ba wai saboda muna kan mulki ba ne, ayyuka da nasarorin da shugaban ƙasa ya samu za su sa ƴan Najeriya su kara ba shi amana karo na biyu a 2027."
- Shugaban ƙungiyar APC a Arewa ta Tsakiya, Saleh Zazzaga.
APC ta maida zazzafan martani ga Peter Obi
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar APC ta caccaki Peter Obi, inda ta ce yana yunkurin tunzura jama'a kan gwamnatin Bola Tinubu.
APC dai ta fusata ne bayan Obi ya zargi Bola Tinubu na yin rufa-rufa kan halin da kasa ke ciki kuma ya bukaci shugaban ya daina yawam tafiye-tafiye.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng