Wike Ya Tsokano Tsuliyar Dodo da Ya Tabo Tsohon Gwamna, Ya Sha Rubdugu
- Dattawan jihar Rivers sun bukaci Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya nemi gafarar kalaman batanci da suka ce ya yi wa tsohon gwamna, Dr. Peter Odili
- An ruwaito cewa dattawan sun bayyana cewa kalaman Wike sun sabawa dabi’un girmama dattawa da mutuntawa da jihar Rivers ta yi kaurin suna da su
- Sun yabawa Odili a matsayin shugaba mai biyayya wanda ya hakura da takarar shugaban kasa a 2007 domin daidaito tsakanin yankin Arewa da Kudu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Rivers - Dattawan jihar Rivers sun yi kira ga Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da ya nemi afuwa kan kalaman da ya yi wa Dr Peter Odili.
Sun bayyana rashin jin dadinsu kan kalaman Wike da suka ce sun sabawa dabi’un dattawa, musamman girmama manya da mutunta gogewarsu.
Vanguard ta ce kiran ya zo cikin wata takarda da dattawan suka fitar wacce manyan jagororin jihar, ciki har da tsohon gwamna Celestine Omehia da Uche Secondus suka sanyawa hannu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zargin Nyesom Wike da batanci ga Peter Odili
Rahoton Arise News ya ce dattawan sun ce kalaman Wike kan Dr Odili, dangane da zargin cewa ya kasa tsayawa takarar shugaban kasa, ba gaskiya ba ne.
A cewarsu, Dr. Odili ya yi biyayya ga umarnin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo wanda ya bukaci ya janye takara domin daidaito tsakanin Arewa da Kudu.
“Dr Odili ba ya tsoron takara. Ya nuna biyayyarsa ga jam’iyyar PDP ta hanyar yin murabus domin marigayi Umaru Musa Yar’Adua ya zama dan takarar shugaban kasa a 2007."
- Dattawan Rivers
Dattawan Rivers sun ja kunnen Nyesom Wike
Dattawan sun bayyana cewa kalaman Wike ba su dace da tsohon gwamna da ke rike da mukami mai girma kamar Ministan Abuja ba.
Sun bayyana cewa a matsayin tsohon gwamna da dattijo, ya kamata Wike ya zama abin koyi wajen girmama dattawa da tsare mutuncinsa a bainar jama’a.
Manyan jihar Rivers sun yabawa Peter Odili
Dattawan sun yabawa Dr Peter Odili a matsayin jagora wanda ya karfafa ‘yan siyasar jihar Rivers da suka hada da Wike.
Sun ce Dr Peter Odili ya gina jagoranci tun daga lokacin da ya kafa wata tafiya a 1998, wanda ya horar da yawancin ‘yan siyasar jihar Rivers har zuwa yau.
An bukaci Wike ya ba Odili hakuri
A karshe, dattawan sun bukaci Wike da ya nemi gafarar Dr Odili kan kalamansa da suka ce sun sabawa mutuncin dattawa da al’adar jihar Rivers.
Sun ce wannan matakin ne kawai zai dawo da martabar Wike da kuma tabbatar da cigaba da zaman lafiya da mutuntaka a jihar Rivers.
Fubara ya lallasa mutanen Wike
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya yi wankin babban bargo ga Nyesom Wike da mutanensa.
A bikin sabuwar shekara, gwamna Fubara ya bayyana cewa shi jan biro ne maganin dakikin yaro, wanda hakan alama ce ta zai cigaba da bugawa da Wike.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng