Dalilin da Ya Sa Gwamnan Bauchi bai Bi Gwamoni zuwa Gidan Tinubu ba
- Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya ce ba siyasa ba ce ta sa bai halarci ziyarar shugaban kasa Bola Tinubu a gidansa ba
- Wasu mutane sun fara zargin gwamnan da rashin halartar taron ne sakamakon sabani da ya samu da Tinubu kan kudirin haraji
- Mai magana da yawun gwamnan ya ce Bala Muhammad yana cikin jimamin rasuwar da aka yi masa ne a ranar sabuwar shekara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya musanta zargin cewa dalilan siyasa ne suka hana shi halartar ziyarar sabuwar shekara da gwamnoni suka kai wa Bola Tinubu.
Gwamnonin Najeriya karkashin kungiyarsu sun kai ziyara ga shugaban kasa a ranar sabuwar shekara a gidansa da ke Ikoyi, Legas.
Punch ta wallafa cewa gwamnatin jihar Bauchi ta warware zargin inda ta bayyana dalilin rashin ganin Sanata Bala Muhammad cikin tawagar gwamnonin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rashin zuwan gwamnan Bauchi gidan Tinubu
Mai magana da yawun gwamnan ya ce rashin halartar gwamna Bala Mohammed ba shi da nasaba da siyasa, amma ya kasance yana cikin jimamin rasuwar mahaifiyarsa ta riko.
Mukhtar Gidado ya ce mahaifiyar gwamnan ta riko, Hauwa Duguri, ta rasu a ranar sabuwar shekara.
A dalilin haka, gwamnan ya kasance cikin juyayi a gidansa na kauye da ke Duguri, yana karbar ta’aziyya daga al’umma.
“Yana daga cikin al’adar gwamna ya mayar da hankali kan iyalansa a irin wannan lokaci, domin tabbatar da cewa an gudanar da dukkan al’amuran juyayi cikin kwanciyar hankali."
- Mukhtar Gidado
Gidado ya ce duk wani yunkuri na danganta rashin halartar gwamnan da sabanin da aka samu tsakaninsa da fadar Shugaban kasa kan kudirin haraji ba shi da tushe.
Gwamnonin da suka kai ziyarar sabuwar shekara
A ranar sabuwar shekara, wasu gwamnoni daga sassa daban-daban na kasar nan sun kai ziyarar girmamawa ga shugaban kasa Bola Tinubu a gidansa na Ikoyi.
Gwamnonin da suka halarta sun hada da Babajide Sanwo-Olu na Legas, Abdullahi Sule na Nasarawa, da Abba Kabir Yusuf na Kano, tare da wasu da dama daga jihohi daban-daban.
Sabanin Tinubu da Yar'adua kan mukami
A wani rahoton, kun ji cewa an bayyana wani sabani da aka samu tsakanin shugaba Bola Ahmed Tinubu da marigayi Umaru Musa Yar'adua.
Shugaba Yar'adua ya ba Bola Tinubu damar rike mukamin ministan kudi amma aka gargade shi kan amsa tayin saboda wasu dalilai na siyasa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng