NNPP: 'Yan Adawa Sun Gano Lagon Karya Tinubu, Sun Ce Mulki zai Dawo Arewa
- Shugaban NNPP na jihar Kano, Hashimu Dungurawa, ya ce mulkin Bola Tinubu na cike da tsare tsaren da suka musguna wa talakawa
- Ya bayyana cewa NNPP ta shirya tsaf domin samun nasara a matakin jihohi da tarayya a zaben 2027, tare da goyon bayan talakawa
- Dungurawa ya ce manufofin gwamnati mai ci sun wargaza tattalin arzikin kasa, kuma akwai bukatar sauya salon shugabancin APC
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano, Hashimu Dungurawa ya yi ikirarin cewa tsare tsaren Bola Tinubu na musguna wa talakawa za su sa ya fadi a babban zaben 2027.
Hashim Dungurawa ya bayyana hakan ne yayin wata hira da manema labarai a Kano ranar Alhamis, inda ya ce ‘yan Najeriya sun gaji da mulkin APC mai cike da matsaloli.
Rahoton Punch ya nuna cewa shugaban ya yi hasashen cewa NNPP za ta samu nasara a jihohi 36 da zaben shugaban kasa a 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NNPP: Abin da zai sa Tinubu ya fadi zabe
Hashimu Dungurawa ya zargi gwamnatin Tinubu da bullo da manufofin da ke kara wa ‘yan Najeriya wahala tun daga ranar da ya hau mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023.
Daily Trust ta wallafa cewa shugaban ya ce daga ranar rantsar da Tinubu, ya fara zubawa ‘yan Najeriya tsare tsaren da suka musguna musu, kamar sun masa wani laifi.
"Da irin wadannan kalubalen da APC ta haifar, babu shakka a 2027 NNPP za ta tabbatar da cire Bola Tinubu daga mulki.
"Kuma sahihin dan dimokradiyya, Dr Rabiu Kwankwaso zai shiga fadar Aso Villa a matsayin shugaban kasa.”
- Hashimu Dungurawa
NNPP ta shirya samun nasara a 2027
Shugaban ya ce jam’iyyar NNPP ta bude ofisoshi da kafa tsare-tsare a dukkan kananan hukumomi da jihohin kasar nan, wanda hakan ya nuna shirye-shiryen ta na samun nasara.
Dungurawa ya ce sun samu nasarori masu yawa a 2024, kuma suna kan turbar samun karin nasarori a 2025.
Ya kuma jaddada cewa gwamnatin NNPP a Kano ta kawo ci gaba mai ma’ana, musamman wajen gina sababbin gine-gine, bunkasa rayuwar al’umma da karfafa tattalin arziki.
Rabiu Kwankwaso zai bi Tinubu zuwa APC?
Dungurawa ya ce babban kalubalen da jam’iyyar ke fuskanta shi ne yunkurin gwamnati mai ci na kafa tsarin jam’iyya daya.
Ya bukaci gwamnatin tarayya da ta bullo da manufofin da za su rage radadin wahalar talakawa domin inganta rayuwar su.
A karshe, ya karyata jita-jitar cewa Rabiu Kwankwaso, jagoran NNPP, yana shirin komawa APC, yana mai cewa wannan kazafi ne da aka kitsa domin rage martabarsa.
An fara shirin yakar Tinubu a zaben 2027
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaba a APC, Salihu Lukman ya fara gangami domin kafa sabuwar tafiya a 2027.
Salihu Lukman ya bayyana cewa a yanzu haka sun fara tattaunawa da wasu 'yan siyasa ciki har da 'yan APC domin kifar da Tinubu a zabe mai zuwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng