Mutane da Dama Sun Samu Raunuka da Aka Tsige Shugabannin Kananan Hukumomi 2
- Rikici ya barke kan shugabancin kananan hukumomi a Edo, inda aka tsige shugabanni biyu bayan canjin gwamnatin jiha
- Daya daga cikinsu, Aminu Okodo-Kadiri ya ce tsige shi da mataimakinsa ba bisa doka ba ne, kuma ya saba ka'idojin dokar kananan hukumomi
- Okodo ya kalubalanci zargin da gwamnati ta yi cewa sun yi sama da fadi da ₦50m yana mai cewa babu wata shaida kan zargin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Edo - Rikicin kananan hukumomi a jihar Edo ya ci gaba da tsananta ranar Talata, inda aka tsige shugabanni biyu.
Lamarin ya faru ne a ƙananan hukumomin Uhunmwonde da Orhionmwon kan zargin sama da fadi na makudan kudi.
An samu rigima kan shugabancin kananan hukumomi
A Owan East, Prince Aminu Okodo-Kadiri ya bayyana tsige shi da mataimakinsa, Hon. Clement Ojebuovbo, a matsayin matakin da bai da tushe a doka kuma haramtacce, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A Uhunmwonde, rahotanni sun nuna cewa mutane da dama sun jikkata bayan harin da wasu mahara suka kai, wanda aka ce 'yan sanda ne suka yi.
A Uhunmwonde, 'yan majalisar sun tsige shugaban majalisar, Hon. Daniel Osariemen, sannan suka maye gurbinsa da Hon. Chuks Isan don hana yunkurin tsige shugaban karamar hukumar, Hon. Newman Ugiagbe.
Shugaban karamar hukuma ya yi fatali da lamarin
Ugiagbe ya bayyana tsige shi a matsayin ba bisa ka’ida ba, yana mai cewa dokar kananan hukumomi ta tanadi kwamitin mutum bakwai kafin a yi tsige.
A bangarensa, Okodo-Kadiri ya ce an yi amfani da sandar majalisa mara inganci, wanda hakan ya saba doka.
“Gwamnan ya yi zargin sama da fadi da ₦50m, amma ba wata shaida kan hakan.”
- Aminu Okodo-Kadiri
Aminu ya kuma ce wasu 'yan majalisa biyu da aka dakatar sun halarci zaman tsige shi ba tare da an sake dawowa da su ba, wanda ya sa ya zama haramtacce.
Majalisa ta tsige shugabannin kananan hukumomi
Kun ji cewa Majalisar dokokin Edo ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi 18 na jihar bisa zargin almubazzaranci da rashin ɗa'a.
Wannan mataki ya biyo bayan wasiƙar da Gwamna Monday Okpebholo ya aika majalisar, yana mai cewa ciyamomin sun ƙi kawo masa rahoton kudi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng