Bayan Martanin Kwankwaso kan Haɗaka, Peter Obi Ya Magantu kan Rade Radin Haduwarsu

Bayan Martanin Kwankwaso kan Haɗaka, Peter Obi Ya Magantu kan Rade Radin Haduwarsu

  • Dan takarar shugaban kasa, Peter Obi ya musanta rade-radin tattaunawar hadaka da PDP, NNPP ko wata jam’iyyar siyasa
  • Obi ya jaddada bukatar hadin kan ’yan Najeriya don fuskantar zaben 2027 tare da kawo sauyi mai amfani
  • Wannan na zuwa ne bayan Sanata Rabiu Kwankwaso shi ma ya yi fatali da rade-radin tattauna batun hadaka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, a zaben 2023, Peter Obi, ya yi magana kan hadakar jam'iyyun adawa.

Peter Obi ya musanta rade-radin da ake yi cewa yana tattaunawar hadaka da jam’iyyar PDP, NNPP ko wata jam’iyya daban.

Peter Obi ya yi magana kan rade-radin hadakar jam'iyyun adawa
Peter Obi ya musanta wani shiri da jam'iyyun adawa kan zaben 2027. Hoto: Atiku Abubakar, Peter Obi, Rabi'u Kwankwaso.
Asali: Facebook

2027: Peter Obi ya magantu kan haɗaka

Obi ya fadi haka ne yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Abuja a safiyar Alhamis 2 Janairun 2025.

Kara karanta wannan

An fara hada kai da wasu 'yan APC cikin tafiyar kifar da Tinubu a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon gwamnan jihar Anambra ya bayyana cewa babu wata yarjejeniya ko hadaka da aka cimma tsakaninsa da kowacce jam’iyya a halin yanzu.

A maimakon haka, Obi ya yi kira ga daukacin ’yan Najeriya da su hada karfi da karfe don fuskantar babban zaben 2027.

Obi yana mai bayyana bukatar hadin kai don kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki da ta jefa al'umma cikin kunci.

“Babu wata tattaunawar hadaka da kowace jam’iyya a wannan lokaci, dole mu mai da hankali kan hadin kai da aiki tare don kawo canjin da ’yan Najeriya ke bukata.”

- Peter Obi

Peter Obi ya sha alwashin gina LP

Peter Obi ya jaddada kudurinsa na gina jam’iyyar LP domin ta yi karfi yayin da ake shirin fuskantar zaben 2027, cewar Vanguard.

Haka kuma, Obi ya nuna damuwa mai tsanani kan tabarbarewar tsaron kasa, yana mai bayyana matsalar a matsayin abin takaici.

Kara karanta wannan

'Akwai kalubale da rigingimu': Malamin Musulunci ya yi hasashen shekarar 2025

Kwankwaso ya yi magana kan hamada

Kun ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP a zaɓen 2023, ya yi martani kan cimma yarjejeniya tsakaninsa da Atiku Abubakar da Peter Obi.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa babu wata yarjejeniya da ya cimma tsakaninsa da su biyu kan wa'adin da za su yi a mulki.

Kwankwaso ya nuna cewa maganar ta ƙona masa rai domin bai kamata a ce dattawa suna faɗin abin da ba haka yake ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.