"Ka Fito Ka Faɗawa Mutane Gaskiya," Peter Obi Ya Kwancewa Tinubu Zani a Kasuwa
- Tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi ya ce gwamnatin Bola Tinubu ba ta faɗawa ƴan Najeriya gaskiyar halin da ƙasar nan ke ciki
- Mista Obi ya ce saɓanin ikirarin shugaba Tinubu, al'amuran siyasa, tattalin arziki da tsaron kasar nan sun kara lalacewa
- Ɗan siyasar ya ce Najeriya ta faɗo daga matsayin kasa mafi ƙarfin tattalin arziki a nahiyar Afirka, ta koma mataki na huɗu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, ya ce al'amuran siyasa, tattalin arziki da tsaro a Najeriya na kara ta'azzara a kullum.
Tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce saɓanin karerayin da gwamnatin Bola Tinubu ke yi wa ƴan Najeriya, al'amura na kara dagulewa a kowace rana.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, Peter Obi ya bayyana haka ne a wata hira da manema labarai yau Alhamis, 2 ga watan Janairu, 2025 a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Obi ya ce a halin yanzu Najeriya na buƙatar kyakkyawan shugabanci wanda zai zama abin koyi ga wasu a sabuwar shekarar 2025.
Obi: 'Gwamnatin Tinubu na ɓoye gaskiya'
"Yayin da muka shiga sabuwar shekara ta 2025, ya zama wajibi a gare ni in yi magana da ku a matsayina na dan Najeriya mai sha'awar ci gaban kasa.
Al’amuran siyasa, tattalin arziki da tsaro a kasarmu na kara tabarbarewa a kullum, sabanin ikirarin da gwamnatin tarayya ke yi cewa abubuwa na ƙara inganta a ɓangarori daban-daban."
"Najeriya na daya daga cikin kasashen da ke fama da talauci a duniya, inda sama da mutane miliyan 100 ke fama da matsanancin talauci da kuma sama da miliyan 150 da ke cikin fatara."
- Peter Obi.
Najeriya ta faɗo a Afirka a mulkin Tinubu?
Tsohon gwamnan ya ƙara da cewa al’amura sun tabarbare sosai a cikin watanni 18 da suka gabata a karkashin wannan gwamnati mai ci.
A cewarsa, Najeriya ta rikito daga matsayin kasa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka a shekarar 2014 zuwa matsayi na hudu a nahiyar, rahoton Vanguard.
Peter Obi ya yi maganar haɗaka
Kun ji cewa Peter Obi ya ce har yanzu ba su ƙulla wata yarjejeniyar haɗa maja da kowace jam'iyyar siyasa a Najeriya ba.
Tsohon ɗan takarar shugaban kasar ya yi kira ga ƴan Najeriya masu kishin kasa su haɗa kai domin karbe mulkin kasar nan daga hannun APC.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng