Korar Kwankwaso daga NNPP da Manyan Abubawa 5 da Suka Faru a Siyasar Najeriya a 2024
Muhimman abubuwa sun afku a siyasar kasar nan a shekarar 2024 da aka yi bankwana da ita, ciki har da gwagwarmayar hada kai don shirye-shiryen zaɓen 2027.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Daga cikin manyan abubuwan da su ka wakana a fagen siyasa akwai gurfanar da gwamnoni a gaban kotu da gwamnatin tarayya ta yi domin kwato hakkokin kananan hukumomi.
Legit ta tattaro wasu daga cikin manyan abubunwan da suka afku a siyasar Najeriya a shekarar da ta kare a ranar Talata, 31 Disamba, 2024.
1. 2027: NNPP, PDP sun kasa hadewa
Wasu jam’iyyun hamayya, ciki har da ADC da PRP, suna tattaunawar haɗin kai don kayar da APC a zaɓen 2027. Amma LP da NNPP sun musanta shiga irin wannan shirin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana ta ce-ce-ku-ce a tsakanin Atiku Abubakar da PDP da Rabi'u Musa Kwankwaso na NNPP a kan maganar dunkulewa wuri guda domin fatttakar gwamnatin APC a kakar zabe mai zuwa.
BBC Hausa ta ruwaito a baya-bayan nan yadda shugaban riko da PDP, Ambasada Umar Iliya Damagum ya ce su na kokarin shawo kan Sanata Kwankwaso ya dawo gida.
2. NNPP ta kori Kwankwaso a 2024
Daily Trust ta ruwaito cewa jam'iyyu fuskanci kalubale a shekarar da ta gabata, daga ciki har da NNPP da tsohon dan takarar shugaban kasa, Rabi'u Musa Kwankwaso ke ciki.
Rikice-rikecen ya kara kamari, har wani sashe na jam'iyyar ya kori Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, yayin da ake ci gaba da samun rikici a reshen jihohi na NNPP
Har yanzu ana fama da rikice-rikicen cikin gida a NNPP, musamman a jihohin Kano, Ogun da Nasarawa, a dai-dai lokacin da jam'iyyar ke kokarin dinke barakarta.
3. 2024: Ganduje ya tsallake shirin tsige shi
Shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya samu tsallake shirye-shirye daban-daban da aka yi na raba shi da kujerar shugabancin jam'iyyar.
Duk da matsin lamba daga wasu ɓangarorin APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ci gaba da zama shugaban jam’iyya tare da goyon bayan Bola Tinubu.
4. An tsige shugabannin majalisa a 2024
A shekarar 2024 ne aka tsige Shugaban Majalisar Dokokin Ogun, Hon. Olakunle Oluomo, bisa zargin manyan laifukan rashawa.
A ranar 23 ga Fabrairu, Majalisar Dokokin Zamfara ta tsige shugabanta, Hon. Bilyaminu Moriki, inda mambobi 18 daga cikin 24 suka amince da tsige shi.
Haka kuma, a ranar 22 ga Mayu, Majalisar Dokokin Kuros Ribas ta tsige shugabanta, Hon. Elvert Ekom Ayambem, kan zargin cin hanci da rashawa.
5. 'Yan majalisa, 'yan siyasa sun sauya sheka
An samu yawaitar sauya sheka tsakanin manyan ‘yan siyasa daga jam’iyyun hamayya zuwa APC mai mulki a shekarar 2024.
Daga cikin waɗanda suka sauya sheƙa zuwa APC akwai tsofaffin gwamnoni na Kaduna da Imo; Ramalan Yero da Emeka Ihedioha.
Sauran sun hada da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Anyim Pius Anyim; da tsohon hadimin Atiku Abubakar na PDP, Daniel Bwala.
A ranar 4 ga Disamba, 2024, mambobi huɗu na Majalisar Wakilai daga LP da ɗaya daga PDP sun sauya sheƙa zuwa APC.
Sun hada da Tochukwu Okere (Imo), Donatus Mathew (Kaduna), Bassey Akiba (Kuros Ribas), Iyawu Esosa (Edo), da Erthiatake Ibori-Suenu (Delta) da sauransu.
6. Gwamnatin tarayya ta maka gwamnoni a kotu
Gwamnatin Tarayya ta hannun Antoni Janar na Tarayya (AGF) ta maka gwamnonin jihohi a kotu saboda gazawarsu wajen bayar da ‘yanci ga kananan hukumomi.
A ranar 11 ga Yuli, Kotun Koli ta bayar da hukunci cewa kananan hukumomi 774 na kasar nan suna da cikakken ‘yancin cin gashin kansu a ɓangaren kuɗi.
Kotun ta hana gwamnonin jihohi 36 rikewa ko amfani da kudaden da aka ware don kananan hukumomin.
Majalisa ta fadi amfanin kudirin Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya shaida wa 'yan Najeriya cewa da zarar an amince da kudirin harajin gwamnatin tarayya, za a ji dadi.
Ya bayyana haka ta cikin sakonsa na sabuwar shekara, inda ya bayyana cewa akwai bukatar a tabbatar da kudirin harajin domin samun warwarewar tattalin arzikin Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng