PDP, Obi Sun ba Tinubu Lakanin Samo Waraka daga Matsalolin Najeriya

PDP, Obi Sun ba Tinubu Lakanin Samo Waraka daga Matsalolin Najeriya

  • Jam'iyyar PDP ta soki kalaman shugaban kasa a jawabin sabuwar shekara da ya aika ga 'yan Najeriya a ranar Laraba
  • Sakataren yada labarai na PDP na kasa, Debo Ologunagba ya ce akwai alamun Bola Tinubu bai san halin da jama'a ke ciki ba
  • A nasu bangaren, tsofaffin 'yan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar da Peter Obi sun bayyana fatansu a kan 'yan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - ‘Yan adawa sun yi kira ga Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, kan yadda ya kamata gwamnatinsa ta yi jagorancin Najeriya a sabuwar shekarar 2025.

Wasu manyan kusoshi a jam’iyyun PDP da LP suna ganin ya zama dole a wannan shekara gwamnatin APC ta dauki matakai na ceton al’umma daga matsalolin da suka dabaibaye su.

Kara karanta wannan

2025: Farfado da tattalin arziki da batutuwa 9 da Tinubu ya yi a sakon sabuwar shekara

Tinubu
Tinubu ya samu shawarwarin tafiyar da Najeriya a 2025 Hoto: Mr. Peter Obi/Bayo Onanuga/Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa PDP ta soki sakon da shugaba Bola Tinubu ya aikawa ‘yan Najeriya, tana mai cewa sakon ya nuna rashin fahimtar matsalolin da kasa ke ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar PDP ta soki shugaba Bola Tinubu

A cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na PDP na kasa, Debo Ologunagba, ya fitar, jam’iyyar ta yi zargin Tinubu da rashin sanin halin da 'yan kasa ke ciki.

PDP ta shawarci gwamnatin tarayya da ta magance matsalolin tattalin arziki, musamman ta hanyar rage farashin man fetur zuwa akalla N350 kowace lita.

"An manta da Arewa," Peter Obi ga Tinubu

A sakonsa ta shafin X, tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, ya zargi gwamnatin tarayya da mantawa da hukumar ci gaban Arewa ta Tsakiya a kasafin kudi.

Ya shawarci gwamnatin tarayya da majalisar dokoki su gyara wannan kuskure domin kawo ci gaba a shiyyar Arewa ta Tsakiya a sabuwar shekarar da aka shiga.

Kara karanta wannan

"Wahalarku ba za ta tafi a banza ba," Tinubu ya aika sakon 2025 ga 'yan Najeriya

Tinubu: Atika ya fadi fatansa a 2025

Tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana fatan cewa shekarar 2025 za ta zama sabon babi na ci gaba ga Najeriya, musamman wajen farfado da tattalin arzikin kasa.

Atiku ya ce:

"Ina addu’ar Allah ya farfado da tattalin arzikinmu domin mu samu ‘yanci daga matsin tattalin arziki."

Abba ya mika bukatar Kano ga Tinubu

A baya, mun ruwaito cewa gwamnatin Kano ta shaida wa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu muhimmancin kara kawo ayyukan bunkasa tattalin arziki da ci gaban al'umar ga jihar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya mika bukatar a lokacin da ya shiga tawagar gwamnonin Najeriya wajen kai gaisuwar sabuwar shekarar, jim kadan bayan watsi da kudirin haraji.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.