PDP: Abin da Ya Kamata Kwankwaso da Ƴan Adawa Su Yi don Kayar da Tinubu a 2027
- Ƴan adawa ba za su iya kayar da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a babban zaɓen 2027 matukar ba su haɗa kai da jam'iyyar PDP ba
- Muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa, Ambasada Umar Damagum ne ya bayyana hakan a wata hira ranar Talata da ta gabata
- Damagum ya ce har yanzu PDP ce kaɗai jam'iyyar da ke kafa gwamnatoci a jihohi duk da ta jima da barin madafun ikon Najeriya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Mukaddashin shugaban PDP na ƙasa, Ambasada Umar Damagum ya ce har yanzu PDP ce babbar jam'iyyar adawa mafi ƙarfi a ƙasar nan.
Damagum ya ce duk wata maja da jam'iyyun adawa za su haɗa matukar babu PDP a ciki, to ba za su iya kayar da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a 2027 ba.
Muƙaddashin shugaban PDP ya bayyana hakan ne a wata hira da sashen Hausa na BBC ranar Talata da ta gabata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zaben 2027: Babu jam'iyyar adawa kamar PDP
Ya ce idan aka jingine APC mai mulki a gefe guda, babu wata jam'iyyar da ke da karfin lashe zaɓe a Najeriya kamar PDP.
Umar Damagum ya bayyana karfin tasirin PDP, inda ya nuna cewa har yanzun jam'iyyar tana da ƙima a lungu da saƙon Najeriya.
Shugaban PDP ya yi wannan furuci ne da yake mayar da martani ga kalaman tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso wanmda ya kore batun haɗa kai da PDP da LP.
Madugun Kwankwasiyya dai ya tabbatar da cewa babu wata yarjejeniya da ya ƙulla da Atiku Abubakar ko Peter Obi na haɗa maja domin kayar da APC a 2027.
Sai dai Umar Damagum ya ce duk da PDP ta koma tsagin adawa a Najeriya amma har gobe ruwa na maganin dauɗa idan aka fita rumfunan zaɓe.
Damagum ya ce:
"PDP ce jam'iyya ɗaya tilo da take iya lashe zaɓe duk da ta bar mulkin Najeriya. Kwankwaso ya sauya sheƙa amma abin tambayar jihohi nawa ya ci a sabuwar jam'iyyarsa?
"Gaskiya a bayyane take, sama da shekaru 20 da suka wuce, PDP ba ta yi ƙasa a guiwa ba, ta rike matsayinta sannan tana samar da gwamnoni da ‘yan majalisa a kowane bangare na kasar nan."
"Ko da jam’iyyu hudu sun cure wuri guda ba tare da PDP ba, ba za su iya cin zabe ba. Dole sai sun haɗa kai da mu."
Jam'iyyar PDP ta buƙaci Tinubu ya kwato N25trn
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta bukaci shugaban ƙasa ya kwato wasu makudan kudi da aka ce wasu shugabannin APC sun danne.
Babbar jam'iyyar adawa ta kuma yi kira ga Bola Tinubu ya yi duk mai yiwuwa wajen dawo da zaman lafiya, rage tsadar abinci da fetur a ƙasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng