Yahaya Bello Ya Yi Magana kan Tsare Tsaren Tinubu bayan Fita daga Kurkuku
- Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya yi kira ga zaman lafiya da hadin kai domin ci gaban jihar da kasa baki daya
- Yahaya Bello ya nemi goyon bayan al’ummar jihar Kogi ga gwamna Ahmed Usman Ododo da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
- Wani matashi a jihar Gombe, Hamza Sa'idu ya bayyanawa Legit cewa Yahaya Bello ba shi da hurumim ba 'yan Najeriya hakuri kan Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kogi - Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana cewa manufofin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu za su kai Najeriya zuwa ga ci gaba da daukaka.
Yahaya Bello ya yi wannan bayani ne lokacin da ya ziyarci fadar Ohinoyin na Ebira a ranar Talata, bayan kotun Abuja ta bayar da belin shi.
Vanguard ta wallafa cewa tsohon gwamnan ya samu rakiyar gwamna Ahmed Usman Ododo da wasu manyan baki yayin ziyarar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yahaya Bello ya yi kira a goyi bayan Bola Tinubu
Yahaya Bello ya nemi 'yan Najeriya su yi hakuri tare da bai wa gwamnatin Tinubu goyon baya domin magance matsalolin da suka hana ci gaban kasar nan.
Tsohon gwamnan ya ce manufofin gwamnatin tarayya za su samar da cigaba mai dorewa idan aka bai wa shugaba Tinubu goyon baya.
Gwamna Ododo ya yaba da aikin Yahaya Bello
Gwamnan Jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo, ya yaba da kokarin Yahaya Bello wajen shimfida kyakkyawan tushe musamman a bangaren biyan albashi.
Ododo ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da hada kan al’ummar jihar tare da tabbatar da cewa an samu ribar dimokuradiyya.
Sarkin Ebira ya yi kira ga zaman lafiya
Sarkin Ebira, Dr Tijani Ahmed Anaje, ya yi kira ga al’ummar Ebira da su zauna lafiya tare da fifita muradun yankin fiye da bukatun kansu.
Sarkin ya yi addu’o’in fatan alheri ga Jihar Kogi tare da kira ga al’ummar jihar su ba Gwamna Ododo goyon baya domin cimma manyan nasarori.
Legit ta tattauna da Hamza Sa'idu
Wani matashi a jihar Gombe, Hamza Sa'idu ya zantawa Legit cewa yanzu shekara biyu ake nema kuma ba lokacin ba da hakuri ba ne, sai dai a fara gani a kasa.
Hamza Sa'idu ya kara da cewa Yahaya Bello ba ya cikin jami'an Tinubu saboda haka ba shi da hurumin ba 'yan Najeriya hakuri.
Bola Tinubu zai kafa kamfani a 2025
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dauki damarar kafa wani kamfani domin saukaka rayuwa.
Legit ta rahoto cewa shugaba Bola Tinubu ya ce za a gina kamfanin ne a shekarar 2025 domin rage tsadar abinci da sauran kayayyaki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng