'Yadda Tinubu Ya Yi wa Buhari Wayo a Zaben Fitar da Gwani na Jam'iyyar APC a 2022'

'Yadda Tinubu Ya Yi wa Buhari Wayo a Zaben Fitar da Gwani na Jam'iyyar APC a 2022'

  • Tsohon hadimin shugaban kasa, Babafemi Ojudu ya bayyana yadda Bola Tinubu ya yi wa Muhammadu Buhari dabara.
  • Sanata Ojudu ya ce Tinubu ya shammaci Buhari a wajen neman tikitin takara a zaben fidar da gwani na APC a 2022
  • Dan siyasar ya ce Buhari bai goyi bayan Osinbajo ko Tinubu ba a zaben fitar da gwani, kuma hakan ya shafi sakamakon

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon hadimin shugaban kasa, Babafemi Ojudu, ya ce Bola Tinubu ya fi Muhammadu Buhari dabara a siyasa.

Ojudu ya ce Buhari bai taba nuna cikakken goyon baya ga Yemi Osinbajo ko Bola Tinubu a lokacin zaben fitar da gwani na APC a 2022 ba.

Tinubu ya yi wa Buhari dabara domin samun tikitin APC
Tsohon hadimin Yemi Osinbajo ya fadi yadda Tinubu ya yi wa Buhari wayo a zaben fitar da gwani. Hoto: Muhammadu Buhari.
Asali: Facebook

Yadda Tinubu ya shammaci Buhari a 2022

Kara karanta wannan

'Tinubu bai dace da Najeriya ba': Hadimin Osinbajo ya fadi mai nagarta da zai kawo sauyi

Ojudu ya yi wannan bayani ne yayin da yake tattaunawa a wata hira da Tribune ta bibiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ojudu ya ce Tinubu ya yi dabara iri-iri don samun tikitin jam’iyyar kuma daga baya ya zama shugaban kasa.

Tinubu ya yi amfani da dabaru domin samun nasara, duk da cewa Buhari bai daidaita kai tsaye kan wanda zai tallafa wa ba, cewar Daily Post.

Wanda shugaba Buhari ya fi so ya gaje shi

“Saboda irin tsarin da muke aiki da shi, na rika cewa a tarurrukanmu cewa duk wani kokari da muke yi kamar ziyartar mutane da jawabi ga wakilai, kashi 40 ne kawai."
“Kashi 60 yana hannun Buhari, sai dai idan Buhari ya tattaro mutanen da ke kusa da shi, gwamnoni da hadimansa, ba za mu cimma nasara ba."
“Buhari bai taba hada kansa da tawagarsa don goyon bayan Osinbajo ba, kuma ina ganin Tinubu ya fi shi dabara ta hanyoyi da dama.”

Kara karanta wannan

'An lalata Najeriya fiye da kima,' An tono wata tattaunawar Akpabio da Tinubu

- Babafemi Ojudu

A lokacin shirye-shiryen zaben 2023, ana ta rade-radin cewa Buhari ya fi son tsohon shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, fiye da Osinbajo da Tinubu.

Hadimin Osinbajo ya soki mulkin Tinubu

Kun ji cewa tsohon hadimin shugaban kasa, Babafemi Ojudu, ya ce shugaba Bola Tinubu bai dace ya jagoranci Najeriya a wannan lokaci ba.

Ojudu ya bayyana cewa Farfesa Yemi Osinbajo zai iya jagorantar Najeriya da basira da hangen nesa fiye da shugaba Tinubu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.