Bayan Shawarar Kwankwaso, 'Dan Majalisar NNPP Ya Fadi Matsayarsa kan Haraji

Bayan Shawarar Kwankwaso, 'Dan Majalisar NNPP Ya Fadi Matsayarsa kan Haraji

  • 'Dan Majalisar NNPP daga Kano, Mustapha Ghali, ya ce Najeriya ba ta shirya don aiwatar da dokar gyaran haraji ba saboda matsalolin tattalin arziki
  • Dr Mustapha Ghali ya bayyana yadda ya ki yarda da tayinwasu da ke neman goyon bayansa ga dokar harajin da ake ta ce-ce-ku-ce
  • Ya ce dokar na iya jawo rashin daidaito tsakanin jihohi, yana mai kare bukatun Arewa da makwabtan Kano

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Ana ci gaba da ce-ce-ku-ce kan dokar gyaran haraji da ke gaban Majalisar Tarayya bayan gabatar da kudirin.

Dan Majalisar Wakilai daga jihar Kano, Dr. Mustapha Ghali, ya ce kasar ba ta shirya aiwatar da sabon tsarin haraji ba.

Dan Majalisar NNPP ya yi fatali da maganar kudirin haraji
Hon. Ghali Mustapha ya ce Najeriya ba ta yi kwarin saukar kudirin haraji ba. Hoto: Dr. Ghali Mustapha Tijjani/Bayo Onanuga.
Asali: Facebook

Hon. Ghali ya magantu kan kudirin haraji

Ghali wanda ke wakiltar mazabar Gaya, Ajingi da Albasu, ya bayyana yadda wasu ke kokarin shawo kansa kan kudirin, cewar The Guardian.

Kara karanta wannan

"Wuce gona da iri," Dattawan Arewa sun ce a biya diyyar wadanda sojoji suka hallaka a Sakkwato

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, sabanin kasashen da suka ci gaba, inda irin wannan tsarin haraji ke aiki, aiwatar da shi a Najeriya yanzu zai iya haifar da matsaloli ga al’umma.

'Dan majalisar NNPP ya kara da cewa, ko da yake wanda ya gabatar da batun ya ce Kano za ta fi cin gajiyar gyaran harajin.

'Dalilin kin amincewa da kudirin' - Hon. Ghali

Hon. Ghali ya ki amincewa da wannan batu saboda rashin daidaito da dokar za ta jawo wa jihohin makwabta.

Ya ce dalilinsa na kin amincewa da dokar shi ne, wadannan jihohin makwabta na Kano sun fi kusa da za su taimaka wa jihar idan ta samu matsala fiye da sauran jihohi, cewar Leadership.

'Yadda ake lallaba ni kan haraji' - Hon. Ghali

Kun ji cewa dan Majalisar Wakilai daga Kano, Dr. Mustapha Ghali ya ce ana son ya shawo kan takwarorinsa a kan ƙudirin haraji.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta yi wankin babban bargo ga gwamnan Bauchi kan haraji

Ya ce wani ƙusa a Kudancin ƙasar nan da ke majalisar ya nemi ya zo a haɗa-kai domin amincewa da kudirin harajin Bola Tinubu.

Sai dai ya ce yana ganin akwai wasu matsaloli da za su sa amincewa da ƙudurin ya zama babbar matsala ga Najeriya a yanzu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.