"Kar Ka Yadda a Zuga Ka," Kwankwaso Ya Gargadi Abba kan Barin Kwankwasiyya

"Kar Ka Yadda a Zuga Ka," Kwankwaso Ya Gargadi Abba kan Barin Kwankwasiyya

  • Tsohon dan takarar shugaban kasa, Rabi'u Musa Kwankwaso ya yaba da jajircewar gwamna Abba Kabir Yusuf
  • Ya ce gwamnan ya bijirewa dukkanin masu kiraye-kirayen da zai raba kansu ta hanyar kin barin tafiyar Kwankwasiyya
  • Sanata Kwankwaso ya kara da cewa masu son kawo tarnaki a tsakaninsu na da wata mummunan manufar siyasa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Tsohon takarar shugaban kasa kuma jagoran Kungiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya shawarci gwamnan Kano kan masu kiran ‘tsaya da kafarka.”

Ya shawarci gwamna Abba Kabir Yusuf da kar ya mika wuya ga matsin lambar siyasa da ke neman ya nisanta kansa daga Kungiyar Kwankwasiyya.

Kwankwaso
Kwankwaso ya jinjina wa Abba Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

A wata hira da aka yi da shi a ranar Litinin a tashar BBC, Kwankwaso ya bayyana cewa nasarar gwamna Abba Kabir Yusuf, nasara ce ga tafiyar Kwankwasiyya baki daya.

Kara karanta wannan

Kwankwasoya gano bakin zaren, ya fadi manufar 'yan Abba tsaya da kafarka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rabiu Kwankwaso ya soki masu adawa da Abba

Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya soki masu adawa da mulki da kuma jagorancin Abba Kabir Yusuf.

Ya bayyana cewa babu yadda za a yi ya rika katsalandan a yadda gwamnan ke jagorancin jihar, ya zargi wasu tsirarun mutane da son raba kansu.

Kwankwaso ya yaba da jajircewar Abba

Tsohon gwamnan Kano, Rabi’u Kwankwaso ya ce duk da wadannan kalubale, Gwamna Yusuf ya ki mika wuya ga matsin lambar cikin gida da waje don ya bar tafiyar Kwankwasiyya.

“Wasu na jiran ya yi kuskure don su yi amfani da hakan a kanmu wajen cimma burinsu na kashin kansu. Ina yabawa gwamnan da ya tsaya tsayin daka kan bakarsa a kan su,” in ji Kwankwaso.

Kwankwaso ya gano masu zuga Abba

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon gwamnan Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa akwai wani boyayyen buri ga masu kiran 'Abba tsaya da kafarka."

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya fadi gaskiya kan cimma yarjejeniya tsakaninsa da Atiku, Peter Obi

Sanata Kwankwaso ya ce masu wannan kira su na son su raba kansu ne, tare da cimma wata manufa ta siyasa da za ta yi wa tafiyar Kwankwasiyyya da gwamna Abba Kabir illa matuka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.