An Gano Dalilin da Ya Sa 'Yan Arewa Za Su Zabi Tinubu a 2027 duk da Dokar Haraji
- Wani fitaccen masanin siyasa, Jide Ojo ya bayyana goyon bayansa ga kudirorin gyaran haraji na shugaba Bola Ahmed Tinubu
- A wata hira ta musamman da Legit.ng, ya shawarci Tinubu da ya tattauna da shugabannin Arewa maimakon a janye kudirin
- Duk da adawar gwamnonin Arewa, Jide Ojo ya jaddada matakan dabarun Tinubu na samun goyon bayan Arewa a zaben 2027
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Duk da korafe korafe daga Arewa, masanin siyasa, Jide Ojo ya shawarci shugaba Bola Tinubu da ya ci gaba da fafutukar aiwatar da gyaran haraji.
Masanin na ganin cewa adawar da Arewacin kasar ke yi ga gyaran harajin ba zai shafi Bola Tinubu a siyasance ba, musamman a zaben 2027 da ke tafe.

Source: Twitter
Masani ya magantu a kan gyaran haraji
A yayin wata hira ta musamman da jaridar Legit.ng a ranar Lahadi, 29 ga Disamba, Ojo ya bayyana cewa amfanin kudirin harajin ya fi illolin sa yawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jide Ojo ya nuna goyon bayansa ga matakin da shugaba Tinubu ya dauka na ci gaba da fafutukar aiwatar da kudurorin gyaran haraji da ke gaban majalisar tarayya.
Ya bayyana cewa kudurorin hudu na dauke da shafuka sama da 400, inda aka fi samun adawa kan karin harajin VAT da tsarin rarraba kudaden harajin.
Fargabar gwamnonin Arewa kan gyaran haraji
Ojo ya ce akwai bukatar Tinubu ya cimma matsaya da masu adawa da kudirin, wanda janye kudirin zai kawar da wannan damar ta tattaunawa.
Har ila yau, ya lura cewa bayan shekarar 2025, za a samu canjin salon siyasa don haka akwai bukatar a aiwatar da duk wani gyara a cikin shekaru ukun farko.
Idan ba a manta ba, gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya ce Arewa ta dauki matsaya kan kudirin gyaran haraji tare da shawartar Tinubu da ya canza tunani kan kudurorin.

Kara karanta wannan
Gwamnan PDP ya ziyarci Tinubu a Legas, an ji abin da suka tattauna a cikin bidiyo
Gwamna Bala ya yi nuni da cewa aiwatar da kudurorin gyaran harajin zai kawo babbar illa ga ci gaban Arewa da al'ummar cikinta.
2027: Tinubu zai samu goyon bayan Arewa
Sai dai, masanin siyasar, Jide Ojo ya ki amincewa da wannan ra'ayi na gwamnan Bauchi, yana mai cewa Tinubu zai ci gaba da samun goyon bayan Arewa har a zaben 2027.
A cewar Ojo, kudirin, wanda aka tsara bayan doguwar tattaunawa, zai inganta tsarin rarraba kudaden haraji, samar da 'yancin kananan hukumomi, da manufofin kudi.
Ojo ya musanta damuwar da shugabannin Arewa ke da ita kan Tinubu a shekarar 2027, yana mai cewa manufofin shugaban za su taimaka a samun nasararsa.
Duk da hakan, ya shawarci Tinubu da ya kula da damuwar da shugabannin Arewa ke da shi kan kudirin gyaran haraji tare da tattaunawa da su.
Sanata ya fadi gatan da aka yi wa Arewa
A wani labarin, mun ruwaito cewa Sanata Ahmed Aliyu Wadada ya karyata zargin da ake yi na cewa shugaba Bola Tinubu na yakar Arewa ta hanyar gabatar da kudirin haraji.

Kara karanta wannan
'Tinubu ba makiyinmu ba ne': Sanata kan kudirin haraji, ya fadi gatan da aka yi wa Arewa
Sanatan daga jam'iyyar SDP a Nasarawa ya ce Tinubu ba shi da mummunan nufi kan Arewa, kuma ayyukansa suna nuna tsayin dakan gwamnati wajen inganta yankin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
