'Na Yi Nadamar Kin Zaɓen Tinubu a 2023': Matashi Ya Fadi Kuskuren da Ya Tafka a Bidiyo
- Wani matashi ya bayyana nadamarsa kan rashin goyon bayan Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2023, yana mai cewa ya yi kuskure
- Matashin ya ce yanzu ya yarda da hangen nesan Tinubu don inganta Najeriya, yana mai yabo ga cigaban da aka samu
- Ya yi alkawarin zaɓar Tinubu a 2027, yana mai gode wa shugabancin da ya haɗa 'yan Najeriya wuri ɗaya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Wani bidiyo da ya yadu a kafofin sada zumunta ya nuna wani matashi daga Najeriya yana nadamar rashin goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2023.
Matashin ya yi nadama matuka na rashin goyon bayan Tinubu a zaben 2023 da ya gabata inda ya zabi Peter Obi.
Matashi ya yi nadamar kin zaɓen Tinubu
A cikin bidiyon da The Nation ta wallafa, matashin ya bayyana cewa ya yi kuskuren zaɓar ɗan takarar jam'iyyar LP, Peter Obi maimakon Tinubu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya nuna kwarewarsa wajen inganta Najeriya da samar da abababan more rayuwa.
"Ina son ba da haƙuri ga duk wani ɗan Najeriya, na yi kuskuren goyon bayan Peter Obi a zaɓen da ya gabata."
"Yau ina cewa na yarda da hangen nesan Shugaba Tinubu, mun ga inda Najeriya take lokacin da ya hau mulki da kuma inda take yanzu."
- Cewar matashin
Matashi ya yabawa salon mulkin Tinubu
A ƙarshe, ya gode wa shugabancin Tinubu wanda ya haɗa 'yan Najeriya wuri ɗaya, yana mai cewa yanzu sun gane muhimmancin samun jagora mai nagarta.
Matashin ya kara da cewa yanzu ya gane girman hangen nesan Tinubu don ci gaban ƙasar.
Ya yi alkawarin zaɓar Tinubu a zaɓen 2027 domin guje wa sake yin kuskuren da ya yi a baya.
Shirin yan adawa kan zaben 2027 da Tinubu
Kun ji cewa yan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar da Peter Obi na nazarin darasin zaben 2023 da ya gudana a baya saboda shirin zaben 2027.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Atiku da Obi suna duba yiwuwar shiri mai karfi domin tunkarar Bola Tinubu a takarar shugaban kasa.
Asali: Legit.ng