Bayan Shafe Shekaru a Kotu, Gwamnonin PDP Sun Sasanta Rikicin da Ke Tsakaninsu

Bayan Shafe Shekaru a Kotu, Gwamnonin PDP Sun Sasanta Rikicin da Ke Tsakaninsu

  • Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa ya yi farin ciki kan sasanta rikicin rijiyar man fetur ta Soku tsakanin jiharsa da Rivers
  • Gwamna Diri ya yaba da kokarin gwamna Siminalayi Fubara wajen warware matsalolin da suka shafi dukiyar Bayelsa da aka rushe a Port Harcourt
  • Gwamna Siminalayi Fubara ya bukaci dawo da hukumar BRACED don karfafa hadin kan jihohin yankin Neja Delta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Rivers - Jihohin Bayelsa da Rivers sun sasanta tsakaninsu kan rigimar rijiyar mai na tsawon shekaru.

Gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri ya nuna farin ciki kan yadda aka sasanta rikicin rijiyar man fetur ta Soku tsakanin jihohin Bayelsa da Rivers cikin lumana.

Gwamnonin PDP sun sasanta rikicin da ke jihohinsu na tsawon shekaru
Jihohin Rivers da Bayelsa sun kawo karshen rigimar rijiyar mai na tsawon shekaru. Hoto: Sir Siminalayi Fubara.
Asali: Facebook

Rivers: An kawo karshen rikicin kan rijiyar mai

The Guardian ta ruwaito cewa Diri ya fadi haka ne yayin wata ziyarar bikin Kirsimeti da ya kai wa takwaransa na jihar Rivers, Siminalayi Fubara.

Kara karanta wannan

Rarara ya yi wa shugaban Nijar wankin babban bargo kan zarginsa, ya tona asiri

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Diri ya ce yana farin ciki yadda gwamnan Rivers ya taimaka wajen dawo da zaman lafiya, tare da janye karar da aka shigar kotu.

Ya kuma yabawa kokarin Gwamna Fubara kan tsayawa game da dukiyar Bayelsa da aka rushe a Port Harcourt, inda ya ce an kusa cimma maslaha tsakanin jihohin biyu.

Diri ya kara jaddada bukatar ci gaba da hadin kai tsakanin jihohin, inda ya tabbatar wa Fubara da goyon bayan gwamnati da mutanen Bayelsa.

Gwamna Fubara ya nemi alfarmar Diri

A bangarensa, Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, ya bukaci Diri da ya dawo da hukumar BRACED don karfafa ci gaban jihohin yankin Neja Delta, cewar Punch.

Ya ce babu bambanci tsakanin jihohin Rivers da Bayelsa, illa saboda tsarin gudanarwa, don haka ya jaddada bukatar zaman lafiya da hadin kai tsakanin jihohin.

Gwmana Fubara ya gwangwaje ma'aikatan jihar

Kun ji cewa Gwamna Siminalayi Fubara na Ribas ya ba da umarnin turawa kowane ma'aikaci alawus na N100,000 albarkacin bikin kirismeti.

Fubara ya amince a bai wa ƴan fansho kyautar wannan kudi daidai da ma'aikata duk domin su yi shagulgulan kirismeti cikin walwala da annashuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.