Wata Shugabar Ƙaramar Hukuma Ta Fusata bayan An Sauke Ta daga kan Mulki
- Shugabar ƙaramar hukumar Egor a jihar Edo ta yi fatali da matakin tsige ta tare da mataimakinta da wasu kansiloli suka yi
- Eghe Ogbemudia ta bayyana cewa wasu mutane daga gefe ne suka kunno mata wuta domin su yi kashe mu raba da dukiyar al'umma
- Ta buƙaci al'ummar karamar hukumar Egor su ci gaba da bin doka sau da kafa, ka da su ɗauki matakin tsige ta da gaske
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Shugabar karamar hukumar Egor a jihar Edo, Hon. Eghe Ogbemudia, ta yi watsi da matakin tsige ta tare da mataimakinta, Franco Osawe.
Ciyaman ta bayyana cewa matakin da kansiloli, waɗanda sune ƴan majalisa a matakin ƙaramar hukuma, suka ɗauka na tsige ta ya saɓawa tsarin doka.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Hon. Eghe ta rattabawa hannu da kanta ranar Juma'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugabar karamar hukuma ta ɗauki zafi
Ta yi zargin cewa akwai wasu jiga-jigai daga waje da suka zuga tsirarun ƴan majalisar su tsige ta domin su samu damar shiga baitul malin ƙaramar hukumar.
Ta kuma yi ikirarin cewa ba ta taka wata dokar kananan hukumomi ba, kuma ba ta taba samun wata tuhuma daga ‘yan majalisar ba.
Eghe Ogbemudia ta ƙara da cewa tsige ta daga mulki tare da mataimakinta ya saɓawa kundin tsarin mulkin ƙasa.
Yadda aka tsige ciyaman a jihar Edo
Shugabar ƙaramar hukumar ta ce:
"Ni ƴar demokuraɗiyya ce kuma mai fafutukar tabbatar da bin doka da oda. Idan kuka duba tarihi na bana sa baki a abin da bai shafe ni ba kuma ba zan taɓa yin katsalandar a ayyukan kansiloli ba."
"Wasu tsirarun kansiloli ne suka zauna suka ce sun tsige ni, kuma ba su da wata hujja ko tanadin dokar da suka dogara da shi a kundin tsarin mulkin Najeriya.
“Ina amfani da wannan dama na yi kira ga al’ummar karamar hukumar Egor su bi doka da oda tare da yin watsi da matakin da wadannan ‘yan tsirarun kansiloli suka yi."
Kotu ta soke matakun dakatar da ciyamomin Edo
Kun ji cewa babbar kotun jihar Edo mai zama a Benin ta maido da shugabannin kananan hukumomi 18 da aka dakatar.
Kotun ta umarci kowa ya tsaya a matsayinsa har sai ta gama sauraron karar da aka shigar gabanta, ta kuma ɗage zaman zuwa watan Fabrairu, 2025.
Asali: Legit.ng