'Siyasa ce': An Zargi Nijar da Neman Hada Gaba Mai Tsanani Tsakanin Yan Arewa da Tinubu
- Hadimin Bola Tinubu a bangaren sadarwa da hulda da jama'a, Daniel Bwala ya yi magana kan zargin Najeriya da Nijar ke yi
- Bwala ya ce zargin da Shugaba Abdourahamane Tchiani na Jamhuriyar Nijar ya yi kan Najeriya da Faransa yaudara ce mara tushe
- Ya yi kira ga 'yan Najeriya da su yi watsi da wannan zargi yana mai cewa makirci ne don haddasa rikici da gaba a Arewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Hadimin shugaban kasa a Najeriya, Daniel Bwala ya soki Shugaban Nijar, Abdourahamane Tchiani kan maganganunsa.
Bwala ya ce zargin da shugaba Tchiani ya yi kan Najeriya game da ta'addanci yaudara ce marar tushe.
Hadimin Tinubu ya caccaki shugaban Nijar
Hadimin Bola Tinubu ya fadi haka ne a cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X a yau Juma'a 27 ga watan Disambar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A martaninsa, Bwala ya bayyana zargin a matsayin makirci don haddasa rikici da haddasa gaba a Najeriya.
Ya ce an kawo wannan magana domin haddasa gaba tsakanin yan Arewa da kuma gwamnatin Bola Tinubu.
Hadimin Tinubu ya ga siyasa a maganganun Tchiani
“Na ci karo da wani bidiyo daga shugaban sojin Nijar, makirci ne mara tushe, wanda ke kokarin haddasa gaba a Najeriya."
“Bayanin nasa ya fito ne daga yanayin da ba shi da mafita kan matsalolin tattalin arziki a kasarsa, kuma yanzu komai ya juya masa baya.”
“Watakila yana hada kai da wasu ‘yan siyasa a Najeriya, ba za ka sani ba, amma gaba daya manufar ita ce haifar da rikici da gaba a Arewa kan shugaban kasa."
- Daniel Bwala
Bwala ya bayyana cewa Najeriya tana taka rawa mai muhimmanci a yankin Afirka ta Yamma wajen bunkasa kyakkyawar dangantaka da makwabtan ta.
Tinubu ya mayar wa Nijar martani
Mun ba ku labarin cewa Gwamnatin Bola Tinubu ta musanta zarge-zarge cewa tana shirin tayar da rigima a makwabciyarta Jamhuriyar Nijar.
Gwamnatin ta ce tana yin duk mai yiwuwa domin tabbatar da samar da alaƙa mai kyau tsakanin kasashen biyu.
Har ila yau, ta musanta cewa akwai sojojin Faransa a Arewacin Najeriya domin kawo tsaiko a mulkin Nijar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng