Tinubu ko PDP: Ministan Abuja, Wike Ya Bayyana Wanda Zai Goyi Baya a Zaben 2027
- Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce a shirye yake ya sake marawa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu baya a zaɓen 2027 da ke tafe
- Tsohon gwamnan jihar Ribas kuma jigon PDP ya ce ko kaɗan bai yi nadamar goyon bayan Tinubu har ya zama shugaban ƙasa ba
- Wike ya kuma yi fatali da zargin da ake yi masa na ƙwacen filaye a Abuja, inda ya ce ya zama dole masu fiyale su yi abin da ya dace
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Ministan harkokin babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya ce zai goyi bayan tazarcen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.
Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas kuma jigo a jam'iyyar PDP ya ce bai yi nadamar goyon bayan Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ba.

Source: Facebook
Yadda Wike ya taimaki Tinubu a 2023
Guardian ta tattaro cewa Wike wanda ya yi gwamnan Ribas na tsawon shekaru takwas a karkashin PDP ya yi wa Tinubu aiki har ya zama shugaban kasa a 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan kafa gwamnati ne shugaba Tinubu ya ɗauko Nyesom Wike, ya naɗa shi a matsayin ministan harkokin Abuja.
A halin yanzu, Mista Wike ya ce bai yi nadama ba kuma a shirye yake yaa ƙara marawa Bola Tinubu baya a zaɓe na gaba, rahoton Vanguard.
Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne a taron bikin kirismeti da PDP ta shirya kuma ya samu halarta a jihar Ribas.
“Ban yi nadama ba, babu wanda zan ba haƙuri kuma idan dama ta zo zan sake maimata hakan (marawa Bola Tinubu baya)," in ji shi.
Abuja: Wike ya yi fatali da zargin kwace filaye
Ya kuma yi watsi da zargin kwace filaye da wasu mazauna babban birnin tarayya Abuja suka yi masa, ya bayyana cewa dole ne a yi abin da ya dace.
Wike ya kara da cewa dole ne wadanda ke da filayen gwamnati su yi abin da ya dace ko kuma ya kwace filayensu, domin a koda yaushe zai tsaya kan doka.
Wani matashi ɗan PDP, Kabir Abdullahi ya shaidawa Legit Hausa cewa a yanzu jam'iyyar ta daina lissafi da Wike.
Ya ce fatan da suke a taron kwamitin zartarwa watau NEC na gaba, za a kori Wike da duk mai mara masa baya a cikin PDP.
Jigon ya ce:
"PDP ta yi kuskure a 2023 da aka ƙi biyan buƙatun tawagar G5, to amma yanzu idan ka duba gwamnan Oyo ne kaɗai ya rage a mulki, sai Wike da ke minista.
"Don haka ni ina ganin lokaci ya yi da PDP za ta jefar da kwallon mangwaro ta huta da ƙuda, a bar batun Wike, a zauna a haɗa kan ƴaƴan jam'iyya domin muna da dama a 2027."
Wike na shirin kwace filayen manya a Abuja
A wani labarin, kun ji cewa Nyesom Wike ya na shirin kwace filayen manyan mutane ciki har da wanda ake zargin na tsohon shugaban ƙasa ne a Abuja.

Kara karanta wannan
"Za a binciko dalili": Tsohon dogarin shugaban ƙasa a Najeriya ya rasu yana da shekara 54
Hukumar gudamarwa ta Abuja watau FCTA ta bai wa masu filayen wa'adi su biya basussukan da gwamnati ke binsu ko kuma su rasa filayen.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

