Sabon Rikici: Jagora a APC Ya Nunawa Ganduje Yatsa kan Shugabanci
- Babbar Kotun Jihar Rivers ta soke zaɓukan jam’iyyar APC da bangaren jigon jam'iyyar Tony Okocha ya gudanar
- Wani jigo a jam’iyyar APC, Chief Eze Chukwuemeka, ya bayyana hukuncin a matsayin nasara ga dimokuraɗiyya
- Kotun ta kuma ci tara ta Naira miliyan 10 ga masu gudanar da zaɓen saboda ƙin bin umarnin kotu tun a karon farko
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Rivers - Wani babban jigo a jam’iyyar APC, Cif Eze Chukwuemeka Eze ya yabawa hukuncin Babbar Kotun Jihar Rivers na soke zaɓukan jiha da bangaren Tony Okocha ya shirya
Cif Eze ya bayyana cewa hukuncin ya kawo cikas ga ƙoƙarin wasu mutane masu neman take dokokin dimokuraɗiyya a jihar Rivers.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Mai Shari’a Godswill Obomanu ne ya yanke hukuncin tare da lafta tara ga bangaren Tony Okocha da ake kallo yana tare da Abdullahi Ganduje.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukuncin kotu kan zaɓen APC a Rivers
Kotun ta yanke hukuncin ne bayan karar da bangaren Chief Emeka Beke ya shigar kan ƙin bin umarnin kotu wajen gudanar da zabuka.
A cewar Eze, zaɓukan da aka gudanar sun kasance cikin rashin gaskiya domin sauya shugabancin bangaren Emeka Beke, wanda har yanzu wa’adinsa bai ƙare ba.
Kotun ta kuma ci tara ta Naira miliyan 10 ga waɗanda suka shirya zaɓen bisa saba wa umarnin kotu.
Zargin rashin adalci daga Ganduje
Daily Post ta wallafa cewa Cif Eze ya zargi shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, da kawo rarrabuwar kawuna a APC tun bayan da ya zama shugaban jam’iyyar.
Ya bayyana cewa ƙoƙarin Ganduje na naɗa kwamitin rikon ƙwarya domin karɓar shugabancin APC a jihar Rivers ne ya jawo rikicin da ake fama da shi yanzu.
Eze ya yi nuni da cewa hukuncin kotu ya tabbatar da wa’adin Emeka Beke a matsayin shugaba har zuwa shekarar 2025, tare da jan kunne ga masu ƙoƙarin tayar da rikicin siyasa.
Okupe ya yi magana kan takarar 2027
A wani rahoton, kun ji cewa fitaccen dan siyasa a Kudancin Najeriya, Doyin Okupe ya yi magana kan zaben 2027.
Doyin Okupe ya ce bai kamata 'yan Arewa su nemi mulki ba saboda alkawarin karba karba da aka yi da Kudu, ya ce ya kamata su jira sai 2031.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng