Ministan Tinubu Ya Fadi Yadda Ya Cire Tsohon Shugaban PDP daga Muƙaminsa
- Ministan Abuja, ya bayyana dalilin da ya sa ya haɗa baki aka cire tsohon shugaban PDP, Prince Uche Secondus daga mukaminsa
- Nyesom Wike ya fadi haka ne bayan Secondus ya ce suna daga cikin makiyansa a jihar Rivers wanda ya bata masa rai
- Ya kuma bayyana cewa ya fi kowane gwamna a gwamnatin Bola Tinubu samar da damar aikin gwamnati ga mutanen jiharsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Rivers - Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana dalilin da yasa ya goyi bayan cire tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Prince Uche Secondus.
Wike ya ce Secondus ya yi kokarin kakaba wa yan Rivers dan uwansa a matsayin gwamnan jihar.
'Secondus ya so kakaba mana dan uwansa' - Wike
Ministan ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi a bikin godiya da PDP ta shirya a Ahoada ta Yamma, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wike ya ce ya goyi bayan cire Secondus saboda ya shirya kakaba dan uwansa, Tele Ikuru, gwamna madadin Siminalayi Fubara.
A cewar Wike, Celestine Omehia ya yi kokarin zama gwamnan jihar Ribas ta bayan fage, amma an hana shi saboda rashin cancanta.
Ministan ya bayyana cewa babu wani gwamna a gwamnatin Bola Tinubu da ya samar da dama ga jiharsa kamar yadda ya yi wa Rivers, The Nation ta ruwaito.
Yadda Wike ya shirya cire Secondus a PDP
"Na kori Secondus a matsayin shugaban PDP lokacin da ya so mayar da dan uwansa, Tele Ikuru, gwamna."
"A yau kuma, yana cewa yanzu mu abokan gaba ne."
"Shi ne wanda ya hana mutumin zama gwamna, ya so dan uwansa ya zama gwamna."
- Nyesom Wike
Wike ya shirya tatsar biliyoyi daga filaye
Kun ji cewa Hukumar gudanarwar Abuja ta fara harin tara Naira biliyan 30 daga manyan kasar nan da kamfanoni da suka mallaki filaye.
A baya dai, Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayar da wa'adin mako biyu ga masu filayen da su biya kudaden da ake biyansu.
Ya bayyana hukuncin da aka shirya dauka matukar masu filaye da kamfanonin su ka yi biris da umarnin da hukuma ta ba su.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng