'Dalilin da Ya sa Atiku da 'Yan Arewa ba za Su Kayar da Tinubu a 2027 ba,' Okupe

'Dalilin da Ya sa Atiku da 'Yan Arewa ba za Su Kayar da Tinubu a 2027 ba,' Okupe

  • 'Dan siyasa a Kudancin Najeriya, Doyin Okupe ya bayyana cewa bai dace Arewa ta sake samar da shugaban kasa a 2027 ba
  • Okupe ya jaddada cewa Atiku Abubakar ya cancanta, amma matsalar da zai fuskanta ita ce tsarin karba karbar Kudu da Arewa
  • Wani matashi dan jam'iyyar PDP, Bilyaminu Yahaya ya zantawa Legit cewa zancen da Okupe ya yi ba a kan tsarin mulkin kasa aka gina shi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon mai magana da yawun shugaban kasa kuma darakta-janar na yakin neman zaben Peter Obi a 2023, Dr Doyin Okupe ya yi magana a kan zaben 2027.

Doyin Okupe ya ce yankin Kudancin Najeriya ne ya kamata ya samar da shugaban Najeriya a 2027.

Kara karanta wannan

Hauhawar farashi: Tinubu ya fadi shirin gwamnatinsa a kan rage tsadar kayayyaki

Tinubu
An kalubalanci takarar Atiku a 2027. Hoto: Atiku Abubakar|Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa Doyin Okupe ya yi bayanin cewa tsarin siyasar karba karba ba zai ba da damar Arewa ta sake karbar mulki ba a hannun Bola Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Doyin Okupe ya yi watsi da takarar Atiku a 2027

Doyin Okupe ya bayyana cewa matsalar da takarar Atiku za ta fuskanta ba shekaru ba ne ko rashin dacewa, matsalar ita ce tsarin siyasa na karba karba tsakanin Kudu da Arewa.

Okupe ya ce Atiku ya gaza nasara a 2023 ne ba domin bai dace ba, kawai mutane sun ji cewa bai dace shugaba Musulmi daga Arewa ya gaji wani Musulmi daga Arewa ba a lokacin.

The Nation ta rahoto cewa Okupe ya kara da cewa Atiku yana da damar tsayawa takara a 2027 amma zai fuskanci irin kalubalen da ya kayar da shi a 2023.

Okupe: Obi zai fuskanci kalubale a 2027

Kara karanta wannan

Bayan tsokacin shugaban BUA, Dangote ya fadi matsayarsa kan matakan Tinubu

Tsohon jigon jam'iyyar LP, Doyin Okupe ya ce Peter Obi na da yancin yin takara a 2027 amma zai yi wuya ya kwace mulki daga hannun Tinubu.

Okupe
Peter Obi da Doyin Okupe. Hoto: Labour Party
Asali: Facebook

Okupe ya bayyana cewa shugaba Tinubu ya fito daga Kudu, yanki daya da Peter Obi kuma yana gudanar da mulki yadda ya kamata, wanda hakan kalubale ne ga Obi.

Legit ta zanta da dan PDP

Wani matashi dan jam'iyyar PDP a jihar Gombe, Bilyaminu Yahaya ya zantawa Legit cewa a tsarin kundin mulkin kasa babu maganar karba karba.

A karkashin haka, matashin ya ce ko dan Arewa PDP ta tsayar takara za su mara masa baya kuma za suna da tabbas din kayar da APC a zaben 2027.

PDP ta kalubalanci Tinubu kan tsaro

A wani rahoton, kun ji cewa PDP ta ce bayanin da Bola Tinubu ya yi a kan halin da kasa ke ciki ya saba da hakikanin halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Karancin takardan kudi: Kungiyar NLC ta dira a kan gwamnatin Bola Tinubu

Jam'iyyar PDP ta ce idan Tinubu da gaske ya ke tsaro ya inganta kuma hanyoyi sun yi kyau to ya kama hanyar Legas daga Abuja a cikin mota.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng