2027: Kwankwaso Ya Kada Hantar Ganduje, Ya Fadi Shirinsa kan APC a Kano

2027: Kwankwaso Ya Kada Hantar Ganduje, Ya Fadi Shirinsa kan APC a Kano

  • Madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana kan shirinsa dangane da jam'iyyar APC a zaɓen 2024 a Kano
  • Tsohon gwamnan na jihar Kano, ya sha alwashin rage tasirin jam'iyyar adawa ta APC a Kano a zaɓen 2027 mai zuwa
  • Kwankwaso ya kuma buƙaci magoya bayansa da su ci gaba da ƙoƙarin ganin jam'iyyar NNPP ta zama babbar jam'iyyar siyasa a Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Kwankwaso, ya faɗi shirin da ya yiwa jam'iyyar APC a zaɓen 2027.

Rabiu Musa Kwankwaso ya yi alƙwarin rage yawan ƙuri'un jam'iyyar APC a jihar Kano yayin zaɓen 2027.

Kwankwaso zai rage tasirin APC a Kano
Rabiu Kwankwaso ya shirya rage tasirin APC a Kano Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Kwankwaso ya tarbi tsofaffin jami'an gwmanatin Ganduje

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karbar wasu tsofaffin jami'an gwamnatin da ta gabata ta Abdullahi Umar Gandune a gidansa da ke Kano ranar Laraba, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

PDP ta ƙara rasa babban Jigo, dan Majalisa ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bakin na sa sun haɗa da tsofaffin kansiloli da kuma manyan mashawarta na musamman da masu ruwa da tsaki daga ƙaramar hukumar Tsanyawa.

Rabiu Kwankwaso ya yaba da ƙwazon da tawagarsa ta yi a lokacin zaɓen 2023, wanda ya sanya jam’iyyar PDP ta sha wuya kafin samun ƙuri’u 15,000 kacal a Kano.

Ya nuna cewa jam’iyyarsa ta NNPP ta samu wannan gagarumar nasara duk da kasancewarta sabuwar jam'iyyar siyasa haɗe da rashin fara yaƙin neman zaɓe da wuri.

Me Kwankwaso ya ce kan APC a Kano?

"Yanzu, lokacin mu ne domin rage tasirin APC. Za mu yi aiki tuƙuru domin ganin an rage musu ƙuri’u zuwa ƙasa da 15,000 a Kano zuwa 2027."

- Rabiu Musa Kwankwaso

Tsohon gwamnan ya jaddada buƙatar sadaukar da kai da haɗa kai domin tabbatar da jam’iyyar NNPP a matsayin babbar jam’iyyar siyasa a Kano.

Ya kuma ja hankalin magoya bayansa da su ci gaba da mayar da hankali wajen samar da sakamakon da zai tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaɓukan da za a yi nan gaba.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya lissafa ayyukan alheri da Tinubu ya shiryawa jihar Kano da Arewa

Kwankwaso ya ziyarci Obasanjo

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagora a jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci Olusegun Obasanjo.

Kwankwaso tare da tsohon gwamnan jihar Cross Rivers, Donald Duke, sun zoyarci tsohon shugaban ƙasan ne a gidansa da ke birnin Abeokuta na jihar Ogun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng