'Ban San Me na Yi ba': Ministar da Tinubu Ya Kora Ta Ce ba Ta Taba Yin Nadama ba

'Ban San Me na Yi ba': Ministar da Tinubu Ya Kora Ta Ce ba Ta Taba Yin Nadama ba

  • Tsohuwar Ministar mata, Barista Uju Kennedy-Ohanenye ta sake magana bayan cire ta a muƙamin Minista
  • Kennedy-Ohanenye ta ce ba ta yi nadama kan ayyukanta ba yayin da take cikin majalisar Shugaba Bola Tinubu
  • Tsohuwar Ministar ta bayyana cewa tana da burin ci gaba da kare muradun Tinubu duk da cire ta daga mukaminta

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohuwar Ministar mata, Uju Kennedy-Ohanenye harkokin mata ta ce ba ta yi nadama kan ayyukan da ta gudanar ba

Kennedy-Ohanenye ya tabbatar da cewa duk da Bola Tinubu ya kore ta, za ta ci gaba da kare muradun gwamnatinsa.

Tsohuwar ministar mata ta magantu bayan cire ta a muƙamin
Tsohuwar Ministar mata, Uju Kennedy-Ohanenye ta sha alwashin ci gaba da kare Bola Tinubu. Hoto: Uju Kennedy-Ohanenye, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Tsohuwar Minista ta fadi ƙoƙarin da ta yi

Tsohuwar Ministar ta yi wannan bayani ne a jiya Laraba 26 ga watan Disambar 2024 yayin wata hira a gidan talabijin na Channels.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: PDP ta jefi Tinubu da kalubalen tafiya daga Abuja zuwa Legas

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyar ta fadi irin kokarin da ta yi lokacin tana Minista inda ta ce ba za ta iya yin abin da ya fi haka ba.

Ta ce ko kadan babu nadama a abubuwan da ta aikata lokacin tana Minista da suka jawo ce-ce-ku-ce cikin al'umma.

'Zan ci gaba da kare Tinubu' - Tsohuwar Minista

Da aka tambaye ta dalilin da yasa shugaban kasa ya sauke ta, Kennedy-Ohanenye ta ce:

“Ba ni da wannan baiwar da zan iya sanin dalilin, kuma na yanke shawarar ba zan ma yi tunaninsa ba.’”
“Abin da ya fi muhimmanci shi ne an cire ni, kuma na koma kan abin da nake yi kafin mukamin minista."
"Ban taba yin nadamar ayyuka da abubuwan da na yi ba lokacin ina minista."

- Uju Kennedy-Ohanenye

Kennedy-Ohanenye ta kara da cewa tana nan daram a kan kare muradun Tinubu a cikin al’umma ba tare da canjawa ba.

Kara karanta wannan

Ajali ya yi: Wata tirela ta murkushe mai adaidaita sahu, bayin Allah sun rasu

Bayan korarta, tsohuwar Minista ta koma kotu

Kun ji cewa Tsohuwar ministar mata da walwalar jama'a, Uju Kennedy-Ohanenye ta koma kotu bayan korar da Bola Tinubu ya yi mata.

A cikin wani bidiyo, ta lashi takobin yakar cin zarafi, musamman a shari’o’in da suka shafi ‘yan Najeriya da ke da rauni.

Wakiltar wata yarinya ‘yar shekara biyar da aka ci zarafinta da tsohuwar ministar ta yi ya nuna jajircewarta na ganin an shimfida adalci

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.